Daga MAHD MUSA MUHAMMAD
Yayin da rashin tabbas na siyasa da tattalin arziki ke ci gaba da jan ra’ayin saka hannun jari a duniya, attajiran Nijeriya suna ƙara komawa Abu Dhabi da Dubai a matsayin wuraren adana dukiyoyinsu, bisa ga sabon rahoton Wealth Report na 2025 na dandalin Multipolitan.
Rahoton, mai taken “Rahoton Arziki na 2025: Tsarin Haraji”, ya sanya Abu Dhabi, Dubai, da Singapore a matsayin manyan wurare guda uku da manyan Nijeriya ke adana dukiyar su, wanda ke nuna irin kwanciyar hankalin da suke samu bayan ajiye dukiyar su a ƙasashen da nufin samun riba.
A al’adance, manyan ‘yan Nijeriya suna neman dabarun saka hannun jari mai ƙarfi da nufin samar da ci gaba cikin sauri.
“Dukiyar da ke kwana cikin rashin tabbas ba dukiya ba ce; haɗari ce,” inji Chee Okebalama, Babban Abokin Hulɗa na Afirka a Multipolitan.
“Biranen kamar Singapore, Abu Dhabi, Doha, Wellington, da Copenhagen suna kan gaba wajen gudanar da haɓaka dukiya da kuma shirye-shirye.
Bayan rabon kadarorin, yanayin ƙasa yanzu ya zama ginshiƙi na tsara dukiya. Nicholas Michael, Shugaban Rukunin Ci gaban Kasuwa a Multipolitan, ya bayyana cewa inda aka adana dukiya na iya zama da muhimmanci kamar yadda ake saka hannun jari.
“Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Singapore ba wai kawai manyan birane ba ne; suna kare dukiya ta hanyar tsantsan kasafin kuɗi da ingantaccen shugabanci.”
