Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta fitar da sanarwa game da alƙaluman hauhawar farashin kaya a Nijeriya.
Hukumar ta ce, hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 21.88 cikin 100 a watan Yuli 2025, daga 22.22 cikin ɗari a Yuni.
Wannan adadi, da ke cikin rahoton ‘Consumer Price Indeɗ (CPI)’ da aka fitar a ranar Juma’a ya nuna faɗuwar farash a Nijeriya.
Rahoton ya nuna cewa wannan shi ne karo na hudu a bana da aka samu raguwar hauhawar farashi a ƙasar da ke fama da matsalar tattalin arziki.
A cewar NBS, hauhawar farashin watan Yuli ya nuna “raguwar kashi 0.34 idan aka kwatanta da hauhawar farashin watan Yuni 2025.”
Sai dai hukumar ta lura cewa, idan aka duba wata zuwa wata, hauhawar ta fi sauri a watan Yuli fiye da a watan Yuni.
Sanarwar ta ce, “Idan aka kwatanta shekara da shekara, hauhawar farashin ta ragu da kashi 11.52 idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Yuli 2024 (33.40).
“A tsakanin wata da wata, hauhawar farashi a watan Yuli 2025 ya kai kashi 1.99, wanda ya fi na watan Yuni 2025 (1.68) da 0.31.
“Hakan na nufin cewa a watan Yuli 2025, ƙimar ƙaruwa a matsakaicin farashi ta fi ƙimar ƙaruwa a matsakaicin farashi a watan Yuni 2025.”
Hukumar ta bayyana cewa abinci da abin sha marar giya, gidajen cin abinci da wuraren kwana, da harkokin sufuri sun fi taka muhimmiyar rawa a ƙididdigar bana.
NBS ta ce, a watan Yuli 2025, hauhawar farashin kayan abinci ya kai kashi 22.74 bisa ɗari a shekara zuwa shekara, ya karu daga kashi 21.97 bisa ɗari.
Ta ce, “Hakan ya faru ne saboda raguwar farashin wasu kayayyaki kamar kayan lambu, wake fari, shinkafa ta gida, garin masara, dawa, garin alkama, gero, da sauransu.”
Rahoton ya kuma nuna cewa matsakaicin hauhawar farashin kayan abinci na shekara guda, daga watan Agusta 2024 zuwa Yuli 2025, ya kai kashi 26.97 bisa ɗari.
