Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya Nijeriya ta ƙaddamar da sabon shirin gyaran fannin ilimi da ta kira ‘BETA’ domin magance matsalar yara da ba sa zuwa makaranta da kuma tabbatar da ingancin tsarin koyarwa.
Ministan ilimi, Dr Tunji Alausa ne ya bayyana shirin a Abuja, inda ya ce shirin zai bai wa iyaye mata tallafin kuɗi domin su tura ’ya’yansu makaranta tare da kula da halartar su a kai a kai.
Ya ce wannan tsari ya haɗa da shirin mayar da yara makaranta tare da hadin gwiwa da hukumar almajirai ta ƙasa.
Bayanin da ministan ya yi ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ɗauki nauyin rajista da sauran kuɗin shiga makarantar yaran.
Ministan ya bayyana cewa shirin BETA zai magance matsalolin da suka shafi ilimi a ƙasar nan ciki har da ƙarancin malamai, tsofaffin manhajoji, da rashin isassun kayan aiki.
A cewarsa, gwamnati za ta sake horar da malamai tare da horar da matasa miliyan 5 cikin shekaru huɗu masu zuwa domin ƙarfafa fannin koyar da sana’o’i da fasaha.
A halin yanzu, malamai 270 na fasaha sun samu horo na zamani a Ibadan, yayin da sama da malamai 6,000 na makarantu masu zurfi suke samun horo kan basirar fasahar zamani.
Ya ce, daga zangon karatu na 2025/2026, ɗaliban makarantun fasaha a jihohi da tarayya za su samu ilimi kyauta, ciyarwa, ɗakin kwana, da kuma tallafin kuɗi na N22,500 a kowane wata.
Alausa ya bayyana cewa sama da Naira Biliyan 80 aka ware domin gyaran makarantun gama-gari da kuma sabunta makarantu 38 na fasaha a faɗin ƙasa.
Ya ce, an ƙaddamar da shirin STEMM wanda ya shafi ilimin kimiyya, fasaha, lissafi da kuma ilimin lafiya, tare da samar da tallafi har zuwa Naira Miliyan 50.
Ministan ya sanar da ƙarin kuɗin tallafin karatu da za a bai wa ɗalibai a kowane mataki, inda ɗaliban digiri za su samu Naira 450,000, masu digiri na biyu Naira 600,000.
Ya bayyana cewa ɗalibai masu digiri na uku za su samu tallafin karatu na Naira 750,000 a duk shekara.
Bugu da ƙari, an sabunta manhajar makarantu domin ta dace da ƙalubalen ƙarni na 21, ta hanyar ƙara darussa kan tunani mai zurfi, ilimin fasaha, kasuwanci, da ɗabi’a.
