
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMET) ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama da tsawa a faɗin Nijeriya har na tsawon kwana uku, wato daga ranar Litinin zuwa Laraba.
NiMET ta bayyana haka ne ta kafar X, inda ta ce ana tsammanin samun tsawa da matsakaicin ruwan sama a sassan jihohin arewacin Nijeriya da suka haɗa da Jigawa, Zamfara, Kano, Kaduna, Bauchi, Yobe, da Katsina a safiyar Litinin.
A lokacin rana kuma ana sa ran samun ruwan sama a Kebbi, Adamawa da Taraba.
Sannan akwai yiwuwar samun matsakaitan ambaliya a jihohin Bauchi, Jigawa, Katsina, Kaduna, da Kano.
A arewa ta tsakiya kuwa, ana tsammanin hadari da safe a jihohin Neja, Benuwai, Abuja, Filato da Nasarawa, da kuma tsaka-tsakin ruwan sama tare da yiwuwar samun ambaliya a wasu sassan Filato.
A kudanci kuma, ana tsammanin ruwan sama matsakaici a Ondo, Imo, Abia, Enugu, Ibonyi, Anambra, Edo, Delta, Bayelsa, Ribas, Kuros-Riba, da Akwa Ibom.
Har’ilayau, a ranar Talata, hukumar ta bayyana cewa, za a samu hadari da tsawa a sassan Arewa da ruwan sama yankunan Adamawa, Taraba da jihohin da ke maƙotaka da su.
A shiyyoyin tsakiya da kudu za a cigaba da fuskantar matsakaicin ruwan sama a ranar.
Zuwa ranar Laraba, ana hasashen rana a da safe a arewa, sai kuma tsawa zuwa yammaci, yayin da a shiyyar tsakiya kuma za a samu hadari da matsakaicin ruwan sama.
Jihohin kudu kamar su Ibonyi, Akwa-Ibom, Ribas da Kuros-Riba, za a samu yayyafi a safiya da matsakaicin ruwa a lokacin rana, kamar yadda Hukumar ta wallafa.
