Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Sanata Muntari Muhammad Ɗandutse ya jagoranci tawagar yan majalisun tarayya na shiyyar Funtua a jihar Katsina zuwa jaje da bada tallafin Abinci, Siminti, Fitilu masu amfani da hasken rana da Miliyoyin kuɗaɗe ga al’ummar garin Gidan Mantau da ke ƙaramar hukumar Malumfashi waɗanda harin ƴan ta’adda ya shafa.
Sanata Muntari Muhammad Dandutse mai wakiltar shiyar Funtua a Katsina ya jagoranci ƴan majalisun tarayya biyar na shiyar Funtua zuwa garin Ƙarfi dake ƙaramar hukumar Malumfashi domin jajanta ma al’ummar da harin ya shafa.
Tallafin da a ka ba al’ummar ya haɗa da shinkafa buhu dari (100) da masara buhu dari (100) wadda yan majalisun suka bayar sai Siminti buhu dari biyu (200) da kudi Naira Miliyan biyar da sanata Muntari ya samar domin tallafama wanda harin yan bindiga ya shafa a ƙananan hukomomin yankin.
Da yake gabatar da jawabin sa, jami’in hulɗa da jama’a na jamiyyar APC ta Jihar Katsina Hon. Shamsu Sule Funtua ya bayyana cewa wannan tawaga ce wanda tazo domin jajanta masu ƙarƙashin Sanata Muntari Muhammad Dandutse.
Da yake gabatar da jawabin sa Sanata Muntari Muhammad Dandutse ya fara fa jajantama al’ummar da abun ya shafa, tare da basu tabbacin jinin bayin Allah ba zai tafi a banza ba, sanata Muntari Muhammad Dandutse yayi dogon jawabi na irin matakan da gwamnatin tarayya da ta Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Raɗɗa ke ɗauka domin samar da tsaro á jihar.
Sanatan ya sanar da gina sansanin sojoji tare da kawo nau’ikan jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a wannan yanki.
A nasu jawaban na jajantawa ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukomomin Malumfashi da Ƙafur Hon. Aminu Ibrahim da na Musawa da Matazu Hon. Abdullahi Aliyu Janaral sun jajantawa al’ummar garin Mantau bisa iftala’in
da ya faru da basu tabbacin cigaba da ɗaukar matakan ganin zaman lafiya da tsaro ya dawo a yankin
Ƴan majalisar da suka rufawa Sanata Dandutse baya suma sun bada tasu gudunmawa na kayan abinci da kuɗaɗe ga waɗanda hare haren ya shafa.
