An yi kira ga malaman Katsina su yi wa jihar addu’a a watan Mauludi

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamishinan ma’aikatar harkokin addinai na Jihar Katsina Hon. Ishaq Shehu Dabai yayi kira ga malamai da su roƙar ma Jihar Katsina zaman lafiya a wannan wata na Rabiul Auwal.

kwamishinan ya faɗi haka ta bakin babban mai taimakama gwamna akan ɓangaren Ɗarika, Malam Mahe Bello a Katsina wajen taron gudanar da addu”o’i na shigowar watan Rabiul Auwal a babba masallacin Juma’a dake garin Katsina.

A cewar kwamishinan tuni gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya taya al’ummar musulmi na duniya murna zagayowar haihuwar fiyayen halitta Annabi Muhammad SAW.

Malam Ishaq ya tabbatar da cewa gwamanatin Jihar Katsina a shirye take ta tabbatar da an gudunar da bukukuwan mauludi cikin walwala da jin daɗi kamar yadda aka saba a kowace shekara.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga malamai da Shehunai da su yi amfani da wanan dama wajen saka Jihar Katsina cikin addu’a na samun zaman lafiya da kyakyawan shugabanci a jihar.

An gudanar da addu’o’i da nasihohi daga manyan malamai da Shehunnai da suka haɗa da, babban limamin masallacin sarki, Liman Malam Mustapha, Sheikh Hadi Balarabe, Khalifa Sheikh Tijjani Shehu Jafaru, tare da sauran fitattun malamai, sha’irai da Shehunnai da dai sauransu.

By ukarofi