ADC ta buƙaci Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a Katsina da Zamfara kan ƙamarin rashin tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar adawa ta ADC ta kirayi Shugaba Bola Tinubu da ya sanya dokar ta-ɓaci a jihohin Katsina da Zamfara sakamakon munanan hare-hare da ya yi sanadin rasa rayukan sama da mutane 140 a watanni biyu da suka gabata.

A sanarwar da Sakataren yaɗa labaranta, Mallam Bolaji Abdullahi ya fitar, ADC ta bayyana kashe-kashen a matsayin abinda ta kira da koma-baya ga harkar tsaro a Nijeriya, tana mai sukar Gwamnatin Tarayya da gaza samar da mafita a kai.

Jam’iyyar ta kuma yi alla-wadai da kisan masallata guda 30 da aka yi a Ƙaramar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina da ƙone wasu ƴan ƙauye su 20 a gidajensu.

Haka kuma, ta yi ishara da kisan mutane 47 a Zamfara ciki har da guda 38 waɗanda an biya kuɗin fansarsu ga ƴan bindigar da suka halaka su.

Akan haka ADC ta soki Shugaba Tinubu kan abinda ta kira da rashin sanin makama aiki inda ta zarge shi da mayar da hankali akan harkokin ƙasashen waje yayin da matsalolin cikin gida ke cigaba da ta’azzara.

Kazalika, jam’iyyar ta yi tir da taron siyasa na gwamnonin jam’iyyar PDP da aka yi a Zamfara jim-kaɗan bayan kashe-kashen.

By Babaji