
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirinta na miƙa kasafin kuɗin 2026 ga Majalisar Dokoki a watan Satumban 2025 da nufin kawo ƙarshen jinkirin gabatar da shi a ƙurarren lokaci da aka saba yi a baya.
Darakta-Janar na Ofishin Kasafin Kuɗaɗe na Tarayya, Tanimu Yakubu ya sanar da haka a takardar ƙididdige adadin kasafi, wadda ke ɗauke da 7 ga Yuli, 2025 a matsayin kwanan wata, kamar yadda PUNCH ta naƙalto daga shafin ofishin a ranar Lahadi.
An fitar da takardar ne domin sanar da ministoci, manyan sakatarori, shugabannin hukumomi da wasu manyan jami’an gwamnati don su fara shirye-shiryen gabatar da adadin kasafinsu na shekarar 2026.
Ofishin ya kuma ɗauki tsauraran matakai wajen gargaɗin ministocin da hukumomin game haramtattun ayyuka wajen shirya kasafinsu kamar haɗawa da ma’aikatan bogi, ma’aikatan kwangila da kuma ƙara matsayin da ba a tantance ba.
Ya bayyana cewa, za a hukunta dukkan wanda aka samu da hannu a sanya abinda ba ya cikin tsari.
Kazalika, ta gargaɗi ɓangarorin da su tabbatar da miƙa takardun kasafinsu akan lokaci domin bai wa ofishin damar haɗa rahotonsa yadda ya dace.
