Tinubu da ayyukan cigaban ƙasa a jihohin Arewa

Spread the love

Daga SHEHU MUSTAPHA CHAJI

A yayin da muke tunkarar zaɓen shekarar 2027 wasu mutane musamman daga jam’iyyun adawa suna ta yada farfagandar cewa a ƙarƙashin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ana cutar Arewa wajen samar da ayyukan cigaban ƙasa.

In za’a dubi maganganun masu yaɗa wannan farfagandar da ainihin abinda ke ƙasa to za’a fahimci cewa zarge zargen su basu da tushe bare makama. Duk mai bibiya zai fahimci cewa ayyukan cigaban ƙasa da Tinubu ke yi a Arewacin Najeriya sunfi na Kudu yawa.

Shugaba Tinubu yana ƙoƙarin kwatanta adalci na ƙoƙarin ganin cewa kowane yanki a Najeriya na amfana da ayyukan cigaban ƙasa.

Yayin ziyarar da Maigirma Shugaban hukumar raya kogunan Hadejia da Jama’are Engr. Rabiu Suleiman Bichi ya kai jihohin Jigawa da Bauchi ya bayyana wasu daga cikin ayyukan cigaban ƙasa da Shugaba Tinubu ya samar a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi da suke ƙarƙashin hukumar sa. Rabiu Suleiman Bichi yace an kwashe shekaru 26 ana wahalar samun ruwan sha a Dutse babban birnin Jihar Jigawa amma zuwan Shugaba Tinubu ya ware biliyan 60 dan samar da ruwa a Dutse da kewaye. Yace tuni Tinubu ya bada naira biliyan 15 da aka fara da cigaban aikin. Yace (Bichi) ƙarƙashin hukumar raya kogunan Hadejia da Jama’are kawai Shugaba Tinubu ya sahale a kashe biliyan 98 domin gyaran Dam ɗin Tiga da Chalawa Gorge Dam da Kalala Dam da Kafin Zaki Dam da ayyukan noman rani na Kafin Ciri da gyara da kula da Hadejia Barrage da samar da sabbin Kadada dubu 6,500 dan inganta noman rani da wasu ayyukan duk a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi.

In jami’an gwamnati za su yi koyi da Engr. Rabiu Suleiman Bichi wajen bayyana ayyukan dake hukumomin su da farfagandar yan adawa bai zai yi wani tasiri ba.

Akwai ayyukan cigaban ƙasa sabbi da waɗannan aka cigaba da aikin su ƙarƙashin mulkin Shugaba Tinubu. Waɗannan suna kaɗan daga cikin manyan ayyukan cigaban ƙasa da a keyi a Arewacin Najeriya:

  1. Baban titin Sokoto zuwa Badagry da ya ratsa ta jihohin Sokoto da Kebbi da Neja da Kwara mai tsawon kilomita 1068 inda titin zai haɗe da jihohin dake Kudancin Najeriya.
  2. Aikin dasa bututun gas daga Ajaokuta zuwa Abuja da Kaduna da Kano da akafi sani da AKK.
  3. Aikin tagwayen hanyoyi mai nisan kilomita 375 da zai ratsa ta jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina da Kaduna.
  4. Cigaba da aikin titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Kaduna.
  5. Cigaba da aikin titin bypass ɗin Lafiya a jihar Nasarawa.
  6. Gina dubban gidaje a jihohin Sokoto da Kebbi da Neja da Kaduna da Binuwai da Zamfara da Kano.
  7. Cigaba da aikin titin Abuja zuwa Kaduna da Kano.
  8. Cigaba da aikin bypass a gabashin Kano.
  9. Aikin titin Maiduguri zuwa Manguno.
  10. Aikin titin Cham zuwa Numan (Gombe zuwa Yola).
  11. Aikin titin Mil 9 zuwa Oturkpo da Makurdi.
  12. Cigaba da aikin titin Abuja zuwa Lokoja.
  13. Cigaba da aikin titin Akwanga zuwa Jos da Bauchi da Gombe mai tsawon kilomita 439.
  14. Cigaba da aikin titin Kano zuwa Katsina.
  15. Gina sabon titin jirgin ƙasa da zai riƙa zirga zirga a cikin birnin Kano
  16. Gina sabbin tashoshin mota na zamani a jihohin Kano da Gombe da Kogi.
  17. Samar da hukumomin raya yankin Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya.
  18. Aikin tagwayen titi daga Bauchi zuwa Gombe.
  19. Gyara da samar da sabbin tituna guda 135 a Abuja.
  20. Samar da ruwan sha a Abuja.
  21. Samar da ruwan sha a garin Dutse Jihar Jigawa.
  22. Cigaba da aikin titin daya ratsa ta Sahara mai tsawon kilomita 456.
  23. Cigaba da aikin samar da tashar lantarki a Gwagalada da zai samar da megawatts 1350.
  24. Cigaba da aikin titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Dutse da Maradi.
  25. Ayyukan dakatar da zaizayan ƙasa a ƙananan hukumomi 16 a Jihar Kano.

Abubuwan da muka lissafo a sama na daga cikin ayyukan cigaban ƙasa da Shugaba Tinubu ke yi kusan a ko ina a Arewacin Najeriya. Waɗannan ayyukan cigaban ƙasa za su taimaka wajen bunƙasar tattalin arzikin Arewa da Najeriya.

Shugaba Tinubu ya cancanci jinjina dan cigaba da ayyukan cigaban ƙasa da ba’a gwamnatin sa aka fara ba saɓanin halayyar yan siyasa in suka karɓi mulki na ƙin ƙarasa ayyukan cigaban ƙasa da basu suka kirkiro ba.

Akwai bukatar gwamnatin shugaba Tinubu tayi ƙoƙarin daƙile farfagandar yan adawa ta hanyar jawo yan siyasa irin su Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso da mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan masarautu Malam Abbas Tijjani Hashim dan sanar da al’umma ire iren ayyukan cigaban ƙasa da Shugaba Tinubu ke yi musamman a Arewacin Najeriya.

Arewacin Najeriya tabbas na cin moriyar ayyukan cigaban ƙasa ƙarƙashin mulkin Shugaba Tinubu kuma babu abinda za su saka masa fiye da sake zaɓen sa a shekarar 2027.

Amb. Shehu Mustapha Chaji

By ukarofi