Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Masarautar Saudiyya ta gargaɗi alhazai ‘yan Nijeriya da ke shirin zuwa Hajjin shekarar 2026 cewa duk wanda aka kama yana gudanar da ibadar Hajj ba tare da ingantacciyar Biza ta Hajj ba, zai fuskanci tara har Riyal 20,000 (kimanin Naira Miliyan 8.15) tare da ɗaurin gidan yari.
Gargaɗin ya fito ne yayin taron tattaunawa ta yanar gizo tsakanin Hukumar Hajji ta ƙasa (NAHCON) da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya domin duba shirin hajjin na baɗi. Dr. Rania Adham daga Ma’aikatar Hajji ta Saudiyya ce ta jagoranci zaman.
A wata sanarwa da NAHCON ta fitar, ta ce hukumomin Saudiyya sun jaddada wajabcin bin dukkan ƙa’idoji da wa’adin da aka sanya, tare da gargaɗin cewa ba za a yi sauyi ko ƙara su gaba ba.
Wa’adin sun haɗa da: Rattaɓa hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a watan Nuwamba 2025, ranar 4 ga Janairu 2026 a matsayin iyakar lokacin biyan kuɗin masauki da tabbatar da kwangiloli, da kuma 1 ga Fabrairu 2026 don loda kwangilolin sufuri da masauki a dandalin Nusuk Masar. Ranar ƙarshe ta fitar da Biza kuwa za ta kasance 1 ga watan Shawwal.
Hukumomin Saudiyya sun koka kan jinkiri da ake ta fama da shi daga Nijeriya a shirye-shiryen da suka gabata, suna gargaɗi cewa irin wannan na iya shafar jin daɗi da walwalar alhazan Nijeriya.
