Laifina kaɗai shine gyara ɓangaren man Nijeriya, inji shugaban NNPC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A ranar Alhamis ne Babban Jami’in Rukunin Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPCL), Bayo Ojulari, ya nesanta kansa daga siyasantar da ɓangaren mai, inda ya ce ya mayar da hankali wajen yin garambawul da kuma farfaɗo da matatun man ƙasar.

Ojulari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karɓar tawagar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Nijeriya (PENGASSAN), ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Festus Osifo, a hedikwatar kamfanin da ke Abuja.

“Ni ba na ɓoye wa kowa komai. Ni ba ɗan siyasa ba ne, amma na fahimci akwai buƙatar na ƙara koyon wasu dabaru na siyasa.

“To sai dai, sha’ani na gyaran matatun mai wani shiri ne na ci gaban ƙasa, a kan wannan, na shirya yin tuƙuru domin ganin an cimma nasarar farfaɗo da su.”

Shugaban Kamfanin na NNPC ya bayyana cewa kamfanin na ƙara zage damtse wajen farfaɗo da matatun man ƙasar nan da suka lalace da kuma mayar da su zuwa ga cikakken aiki.

Ya bayyana cewa hukumar gudanarwa na tunanin yin amfani da tsarin samar da iskar Gas na Nijeriya (NLNG), wanda ake ɗaukarsa a matsayin nasara a fannin makamashi.

A cewarsa, shirin na gyaran matatar man ya yi daidai da umarnin shugaban ƙasa Bola Tinubu na maido da aikin tace man Nijeriya da rage dogaro da albarkatun man fetur da ake shigowa da su daga aasashen waje.

Ojulari ya kuma nuna fargaba kan barazanar da ake yi wa rayuwarsa da na wasu manyan jami’an hukumar ta NNPC, yana mai alaƙanta wannan ƙiyayya ga wasu muradu masu adawa da garambawul ɗin da yake yi.

“Babban laifina shi ne sauye-sauyen da muka ɓullo da su daidai da umarnin shugaban ƙasa na farfaɗo da matatun mai, wasu manyan buƙatu suna shirin kwance min kujera, amma na jajirce,” inji shi.

Ojulari ya yi kira ga ’yan ƙasa da ma’aikatan kamfanin da su ci gaba da goyon bayan gyare-gyaren da NNPCL ke yi.

Ya bayyana cewa nasarar farfaɗo da matatun mai zai rage dogaro da shigo da mai daga waje, tare da sauƙaƙa wa talakawa a harkar sufuri da wutar lantarki.

By ukarofi