Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya ce ba zai tsaya takarar kowanne irin muƙami ba a zaɓen 2027, inda ya ce burinsa kawai ya samar wa jiharsa da Nijeriya nagartattun shugabanni.
Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Kaduna, lokacin da ya karɓi wasu matasa ƙarƙashin jagorancin Aliyu Bello da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar haɗakar ’yan adawa ta ADC.
El-Rufa’i ya kuma soki lamirin gwamnati mai ci, inda ya ce ’yan Nijeriya na ganin gazawarta ƙarara ba tare da wani ya musu ƙarin bayani ba.
“Ba abin da wannan gwamnatin ke yi ban da karya a kullu-yaumin. Kowa ya san gaskiya. Ni ba na neman kowacce irin kujera. Ba zan tsaya takarar Sanata ba ko ma kowanne irin matsayi, shi ya sa nake rokonku da ku zo mu hada hannu mu kori azzalumai,” in ji shi.
Ya ce a baya abin da ya tsara shi ne bayan ya sauka daga Gwamna zai yi ritaya daga harkokin siyasa gaba daya, amma abubuwan da ke faruwa ne suka tailasta masa dawowa, kodayake babu buƙatar kashin kansa a ciki.
Tsohon Gwamnan ya ce burinsa shi ne ya taimaki matasa da mata da masu rajin kawo ci gaba domin su karɓe ragamar siyasa su kawo canjin da ake buƙata.
Daga nan sai ya buƙaci mutane da su je su yi rajistar zaɓen da aka fara domin shiga harkokin zaɓe ka’in da na’in.
