Gwamnatin Zamfara, UNICEF da ƙungiyoyi sun yi bita kan yara marasa galihu

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Ƙungiyar kare haƙƙin yara ta ƙasa tare da tallafin ƙungiyoyin SOS, UNICEF da ma’aikatar kula da mata da ci gaban al’umma ta jihar Zamfara sun gudanar da taron kwanaki biyu na masu ruwa da tsaki kan nazari da tabbatar da ƙa’idojin tattaro bayanan ingantattu da za a kula da su don kula da yara musamman marasa galihu a jihar.

Da take jawabi yayin taron bitar a ranar Lahadi, kwamishiniyar ma’aikatar mata da ci gaban jama’a ta jihar, Dakta Aisha MZ ta bayyana ƙudurin gwamnatin jihar na yin haɗin gwiwa da duk wata ƙungiya mai zaman kanta da ke son kawo ci gaba mai kyau da zai amfani al’ummar jihar.

“Gwamnatin Zamfara ta inganta harkokin kiwon lafiya, ilimi, da ababen more rayuwa domin ci gaban al’ummar jihar, a shirye gwamnatin jihar take don aiki da duk wata ƙungiya mai son kawo cigaban al’umma”.

Kwamishinan ta ci gaba da cewa gwamnatin jihar ta gina makarantun almajirai masu inganci a gundumomin sanatoci uku domin haɓaka ilimin addinin musulunci da na ƙasashen yamma.

A nata jawabin, babbar darakta ta fannin kula da yara a ma’aikatar, Hajiya Farida Abdulrazak Tigana ta ce maƙasudin bitar daftarin a jihar, shi ne nemo hanyoyin da za a bai wa yara marasa galihu kulawa ta musamman a gwamnatance.

Ta kuma nemi masu ruwa da tsaki da su shigar da sunayen yaran da ba a gano iyayensu ba, marayu da sauran waɗanda basu da ƙarfi.

“Manufar wannan taron shine a tabbatar da kariya da jin daɗin yaran da ba su da kulawar iyaye ko kuma ke cikin halin matsalar tattalin arziki da kulawar iyaye su”.

A nasa jawabin, Farfesa Umar Alƙali, ya yi kira ga gwamnatin Zamfara da ta tabbatar da ɗorewar aiwatar da bitar da kuma samar da ingantattun manufofin kulawa ga ƙananan yara marasa ƙarfi.

By ukarofi