
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ƴan sanda a Jihar Kaduna ta ce ta ƙaddamar da bincike akan tarzoma da aka tayar a wani taron siyasa da aka alaƙanta da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i.
An samu rahotannin harbe-harbe da hayaniya a yayin gudanar da taron.
A cewar rundunar, al’amarin ya faru ne a lokacin da jam’iyyar adawa ta ADC ta ke tsaka da taro ba tare da sanar da hukumomin tsaro ba gabanin farawa duk an sha gargaɗi akan haka.
Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan a wata takarda, ya ce bincike ya nuna cewa an yi zargin wasu ƴan daba da ƴan kanzagin siyasar tsohon gwamnan ne suka ta da rikici a taron, lamarin da ya yi sanadin raunata wasu da jefa da dama cikin firgici.
Yayin da hukumar ta binciki Sakatariyar ADC, shugabancin jam’iyyar ya musanta hannu a taron da nesanta kansa daga ikirarin El-Rufa’i, yana mai jaddada aniyarsu na cigaba da kiyaye doka da oda.
Kazalika, rundunar ta ce tana cigaba da gudanar da bincike akan al’amarin, inda duk wanda aka samu da hannu a ciki, zai fuskanci hukuncin doka.
Haka kuma, ta gargaɗi masu otal da wuraren taruka da su riƙa tabbatar da tantance tarukan siyasa da makamantansu daga hukumomin tsaro kafin bada dama ga masu taro.
