Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon Sufeton ƴan sanda, Solomon Arase ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Sufeto-Janar na ƴan sanda, Solomon Arase ya rasu.

Wani daga ciki mataimakansa ya tabbatar wa Blueprint rasuwar marigayin a yau Lahadi.

A watan Afrilun 2015 tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya naɗa shi a muƙamin, sannan ya yi murabus a 2016.

Ya kuma cigaba da yi wa ƙasa hidima a matakai daban-daban tun daga lokacin.

Haka ma a watan Janairun 2023, ƙarƙashin shugabancin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, an naɗa shi Shugaban Hukumar Ƴan Sanda PSC, inda ya riƙe muƙamin har zuwa watan Yunin 2024.

By Babaji