Siyasar Nijeriya ta bambanta da siyasar kowacce ƙasa a duniya, yanda ake yinta da kuma yanda ‘yan siyasar suka maida ita wani al’amari da kai-tsaye za a kira da ‘Ko a mutu, ko ayi rai’, domin siyasa ce da kwata-kwata ta sauka daga kan ainahin turba ta dimokraɗiyya.
Dalilaina suna da yawa na faɗin haka, saboda yadda ‘yan siyasa suke taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar matasa a sha’anin siyasa. Ko shakka babu, ‘yan siyasa sun lalata matasa da dama, sun gurɓata rayuwarsu tun lokacin da ake ganin akwai ƙarancin wayewa, da ma yanzu da ake ganin al’umma ta waye sosai-da-sosai.
A duk lokacin da aka buga gangar siyasa, to akwai ‘yan siyasar da suke ɗaukar harkar siyasa tamkar wani yaƙin ƙwatar ‘yanci a tsakanin ƙasa-da-ƙasa don maganin abokan gaba. Da haka suke amfani da matasa ‘ya’yan masu ƙaramin ƙarfi (talakawa), su basu kayan maye ko kuɗin da zasu je su sayi kayan mayen. Za su sha ƙwaya su fito da makamai suna yaƙe baki a titi suna kururuwar sai wane, amma babban abin mamaki shi ne, ba zaka taɓa ganin ‘ya’yansu a cikin matasan da suke masu bangar siyasa ba, me yasa? Saboda sun fifita ‘ya’yansu a kan ‘ya’yan talakawa. Wannan shi zai tabbatar maka da cewa ba za su taɓa adalci ba idan suka hau kujerar mulki.
‘Yan siyasa suna adawa da junansu a zahiri, suna gwara kan mabiyansu, amma duk lokacin da zasu haɗu a waje ɗaya, to zaka gansu suna raha da dariya da juna ana tafawa. Ga duk mai tunani sai ya fahimci cewa sun maida mutane sakarkaru, gidadawa da basu san ciwon kansu ba. Siyasar shirme da hauka ita ce siyasar Nijeriya, siyasar zubar da jinin al’ummar, siyasar binne-binne da tsafe-tsafe, siyasar mafiyanci da shirka da rashin mutunci sai siyasar Nijeriya.
A Nijeriya babu abinda aka fi damuwa dashi a tsakanin masu mulki kamar lokacin zaɓe, lokacin da ake fito da kuɗi da makamai, lokacin da ake fito da runduna-runduna ta jami’an tsaro.
Kowanne ɗan siyasa barinsa a ce shi ne ya lashe zaɓe, ko an zaɓe shi ko ba a zaɓe shi ba. Mafi yawancin su, sun yarda a take, a buge, a karya, a targaɗa, a yanke a kashe al’umma don buƙatarsu ta biya ba wani abu ba ne wannan. Ai ana gani kuma ana ji, akwai waɗanda suke fitowa suna yin maganganu na rashin imani, da rashin hankali da tunani, su ce ko da tsiya, koda tsiya-tsiya sai sun ci zaɓe. Yanzu don Allah ina hankali ko imani ga duk wanda zai yi irin wannan furucin a kan sha’anin da mataki biyu ne, ko ya kai mutum aljanna ko wuta?
‘Yan siyasa za su shiga ƙauyuka neman ƙuri’ar mutanen karkara, za su same su basu da hanya mai kyau, ba wutar lantarki, ba makarantu masu kyau, idan ma akwai babu ingantaccen ilimi, ba ruwan sha, babu asibiti, idan kuma akwai ba magani ko likitoci da zasu duba mutanen ƙauyen.
Noma da kiwo ne sana’ar duk wani mutumin karkara, ba ya samun wata kulawa daga gwamnati. Amma a haka idan yayi noma ya ɗauki kayan gona zai kai kasuwa, sai jami’an tsaron da ke kan hanya sun karɓi kuɗi a hannunsa saboda kayan da ya noma ya ɗauko zai kai kasuwa, sannan idan yaje kasuwar sai ya biya kuɗin shigar da amfanin gonarsa inda ake sayarwa.
‘Yan siyasa zasu yi alƙawurra ga talakawa da sunansu na wakilansu, su faɗa musu cewa idan sun zaɓe su zasu gina rayuwarsu da abubuwan more rayuwa, amma da zarar suka cika muradansu na hawa kujerar mulki sai su manta da mutanen da suka yi wa alƙawari kuma suka zaɓe su (musamman mutanen karkara da ake mantawa dasu sai wani zaɓen ya dawo).
‘Yan siyasa suna haddasa gaba da faɗa a tsakanin mabiyansu, abinda ke haifar da zubar da jini da kisa a tsakanin al’umma, hatta wanda bai ji bai gani ba hakan na shafar sa. Amma har yanzu suna kiran siyasar Nijeriya da sunan Dimokraɗiya. Ni kuma a ganina wannan ba ita ce dimokraɗiya ba, bai kuma kamata a kira hakan da sunan Dimokraɗiya ba, kawai ta’addanci za a ce.
Siyasar Nijeriya ba komai ba ce face ta’addanci, domin siyasa ce ake yi ta zubar da jini da salwantar da rayuka da dukiyar al’ummar ƙasa, jefa rayuwar matasa cikin shaye-shaye, faɗan daba da sata gami da fashi da makami. Domin idan har da gaske ne ‘yan siyasa suna son ci gaban matasa a ƙasar nan, to ya kamata idan suka yi amfani dasu suka cika gurinsu, to su samar musu da aikin yi domin su inganta rayuwarsu, ba wai su ƙyale matasan suna zaman kashe wando a ƙofar manya-manyan gidajensu zaman maula ba, ko zaman shaye-shaye da caca da tara mata a ofisoshin jam’iyya ba.
Wallahi duk wani ɗan siyasa a Nijeriya, ko ka taɓa hawa kujerar mulki ko baka taɓa ba, matuƙar ka taɓa bada wata gudummawarka wajen lalata ‘ya’yan al’umma, to wallahi ka sani cewa zaka tsayu gaban Allah ranar Alƙiyama, kuma sai ka bada ba’asin dalilin hakan. Kai ma kasan cewa baka yi gaskiya ba, domin ka inganta rayuwar ‘ya’yanka, sun yi karatu, ga ƙaton gida, ga babban aiki da babban matsayi, suna rayuwar farin ciki da jin daɗi, ga kuɗi ka tara musu a bankuna da gida, ga tarin kadarori a gida da ƙasashen Turawa, hatta da abinci na ƙasar waje suke ci, idan basu da lafiya a kai su ƙasar Turai a duba lafiyar su, kuma duk da kuɗin al’umma. Amma ‘ya’yan talakawa da ku ke amfani dasu a lokacin siyasa ku cika burinku, sun kasa samun daidai da Paracetamol kyauta a asibiti, ba wai maganar ma a duba lafiyarsu kyauta ba.
Duk ma wanda bai sani ba ya kamata ya sani, wallahi koma-bayan taɓarɓarewar komai a ƙasarmu Nijeriya ‘yan siyasa ne, su ne suka lalata mana ƙasa. Suka kawo mana ƙabilanci da rarrabuwar kawuna, bayan sun haifar mana da talauci. Domin da siyasa suke amfani su hau kujerar mulki su zama shugabanni su riƙa satar kuɗin ƙasa, shi yasa duk wanda yake siyasa ba ya bari sai idan mutuwa yayi. Sun maida siyasa kasuwanci, sun maida zubar da jinin al’umma ba a bakin komai ba. Ana kashe talakawa basu damu ba, ana tayar da Bama-bamai ko a jikinsu, ana garkuwa da mutane suna taron siyasa da abinda ya shafe su.
Yau idan akwai abinda yake hana ‘yan siyasa barci cikin kwanciyar hankali, to bai wuce maganar faɗuwa zaɓe ba. Zaɓe da hawa kan kujerar mulki ne a gabansu don su tara kuɗi suyi suna, suyi yawo a sassan duniya, su gina manyan gidaje da kamfanoni, su sayi jiragen ruwa da zuba hannun jari a bankunan gida da ƙasashen waje, amma ba wai suna yin siyasa ko neman hawa kujerar mulki don su gina ƙasa da al’ummar ƙasa ba, wallahi tallahi, na rantse da Allah Maɗaukakin Sarki da ya busa min numfashi, ba don gina ƙasa da al’ummar ƙasa ba ‘yan siyasa ke neman takara su zamo shugabanni ba.
Tunda kuwa haka ne, ina kira da babbar murya cewa, kowa ya san ciwon kansa. Talakawa (musamman matasa), don Allah mu dawo daga rakiyar ‘yan siyasa, mu ajiye bangar siyasa. Mu sani cewa Allah ne ya halicce mu, kuma rayuwarmu tana hannunSa. Don haka idan mun rasa abinci Shi zai bamu, idan bamu da lafiya sauƙi na gareShi. Allah Shi ne Al-Hayyu rayayyen Sarki da baya mutuwa, kuma shi ne Arrazzaƙu Mai azurta bayinSa.
Ku kuma ‘yan siyasa ku sani cewa, akwai ranar tsayuwa gaban Allah. Wallahi-tallahi, Allah ba zai taɓa barin haƙƙin duk wanda ku ka zalunta ya tafi a banza ba. Za a yi hisabi, kuma Allah adalin Sarki ne, duk wanda yayi zalunci ba zai bar shi ba. Idan a nan duniya kuna ganin kuna yin abinda ku ke so a lokacin da ku ke so, kuma babu wanda ya isa ya taka ku, to ranar tsayuwa gaban Allah babu wanda ya isa ya kare ku.
Rayukan da ake zubar wa a kan harkar siyasa ya isa haka, shugabanni masu riƙe da madafun iko, amanar da ku ka ɗauka ta kare rayuka da dukiyar al’umma, amma kun bari ana cin zarafin al’umma, ana musu kisan gilla tamkar kiyashi.
Kun hana jami’an tsaro suyi aikinsu yadda ya kamata, kun siyasantar da komai. Kotuna sun sama ‘yan siyasa, Alƙalai sun zama ‘yan siyasa, jami’an tsaro sun zama ‘yan siyasa, sarakuna sun koma sarakunan siyasa, Malaman addini sun zama ‘yan siyasa, hukumomin kare haƙƙin ɗan Adam sun zama ‘yan siyasa, dokar ƙasa ta zama ta siyasa. Komai ya zama siyasa a Nijeriya, babu abinda bai zama siyasa ba. Shi yasa kullum al’amura suke ƙara taɓarɓarewa, suke lalacewa, talakawa suna shan wahala su da ‘ya’yansu.
Don haka, ‘yan siyasa kun ci amanarmu, kun ha’inci Allah kun ci amanar Manzon Allah, Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wasallam), kun ci amanar ƙasa. Don haka kuji tsoron Allah, zaku mutu kamar yanda kowa ke mutuwa, kuma za a binne ku a cikin ƙasa ba tare da matsayin siyasa ko wata dukiya da muƙamin da kuke dashi ba, sannan idan an tashi alkiyama zaku tashi tare da mutanen da ku ka yi wa siyasa, ku ka mulke su.
Ba zan yi shiru ba, ba zan fasa faɗar gaskiya ba, kuma ina fatan na mutu a kan gaskiya domin ita ce kowanne mutum Musulmi mai imani nagartacce yake fatan ya mutu a kai.
Bissalam.Daga NAFIU SALISU.
(Marubuci)[email protected]. Kano, Nijeriya.
