A baya ina ganin kamar Ɗankwairo ya fi Shata iya waƙa – Salma Sa’id 

Spread the love

Ina da burika sosai a kan waƙoƙin gargajiya – Salma Sa’id

Daga MUKHTAR YAKUBU

A rayuwa Allah ya kan samar da wasu daga cikin mutane masu basira a fannoni daban daban walau a cikin yara ko a cikin manya.

Salma Sa’id tana daga cikin yara ‘yan baiwa masu fasahar waƙa. Sai dai ita fasahar da take da ita ta daban ce a fagen waƙa. Domin kuwa fasahar da take da ita tana ɗaukar waƙoƙin gargajiya irin na su Shata da Dankwairo da sauran mawakan gargajiya ta rera.

Wannan ya ba ta damar samun gayyata daga manyan makarantu da jami’o’i idan suka shirya taro musamman kan abubuwan da suka danganci Hausawa da kuma al’adun gargajiya.

Ganin yadda ta yi fice a wannan fannin ne wakilinmu ya nemi jin ta bakin ta, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance:

MANHAJA: Da farko za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatun mu.

SALMA SA’ID: To Assalamu alaikum. Da farko dai suna na Salma Sa’id kuma an haife ni a garin Kaduna a shekarar 2011 a nan na fara Makarantar Islamiyya da boko. Sannan sai muka dawo garin Kano, a inda na ci gaba da karatuna a nan Kano wanda a yanzu ina ajin farko na babbar sakamdare, kuma a ɓangaren Alkur’ani, Ina ajin masu bin ‘yan sauka.

Kina da wata baiwa da Allah ya yi miki ta kwaikwayon waƙoƙin gargajiya na tsofaffin mawaƙa kamar su Shata da Dankwairo da sauran su. Ko ya aka yi kika samu kanki a wannan fage?

E to na fara ne sakamakon ina yawan jin waƙoƙin gargajiya. Ganin yadda abin ya yi mini tasiri ne ya sa mahaifiyata ta ga dacewar da ɗora ni a kan hanyar da zai zama na yi amfani da wannan damar wajen gina rayuwa ta. Don gaskiya ina da son waƙoƙin gargajiya sosai.

Duk da kina son waƙoƙin gargajiya, a yanzu da kike yi wanne waƙoƙin kika fi karkata wajen rairawa?

To gaskiya dai na fi karkata ga waƙoƙin Shata, saboda, a baya ina ganin kamar Dankwairo ya fi Shata iya waƙa, saboda na ji waƙar sa ta Sarkin Muri, amma daga baya da na zurfafa a kan jin waƙoƙin Shata, sai na ji ai dukkan su ma ya ma fi su iya waƙa.

To baya ga waƙoƙin Shata wanne waƙoƙin kike rerawa?

Ina rera waƙoƙin Shata, Dankwairo, Sani Aliyu, Dandawo, Ali Makaho, Uwani Zakirai, Sani Sabulu, da dai sauran mawaƙan gargajiya.

Wani abu da zai baiwa mutane mamaki a matsayin ki ta mace akwai waƙoƙin gargajiya na mata ko me ya sa ba ki karkata ba wajen yin su sai na maza?

E gaskiya ne. Amma ni a yadda nake gani, sai na ji waƙoƙin mazan sun fi na matan daɗi, kamar dai Barmani Coje ka ga ban cika jin waƙoƙin ta sosai ba, saboda mahaifiyata ta ce ba zan fara jin waƙoƙin Barmani Coje ba a yanzu ina ƙarama. Har gara ma dai Uwani Zakirai ina da littattafan ta Ina karanta tarihinta da waƙoƙin ta .

To kamar Magajiya Danbatta da Uwaliya mai amada fa?

Gaskiya su waɗannan ban ma san su ba.

Ko kina da tunanin faɗaɗa waƙoƙin ki nan gaba ki haɗa har da na mata?

E to zan fara haɗawa da su nan gaba, don haka zan je na yi bincike a kansu.

Tarukan da kike zuwa a manyan makarantu, ana gayyatar ki ne ko kina zuwa ki gabatar da kanki a matsayin mawaƙiya?

A’a, ana gayyata ta ne, don gaskiya an gayyace ni tarurruka masu yawa a manyan makarantu kamar B U K sun sha gayyata ta idan sun shirya tarukan Hausa da sauran manyan makarantu.

Ko me ya fi burge ki idan kin je wajen taro?

Ni abin da ya fi burge ni shi ne yadda mutane suke ƙarfafa mini gwiwa da tafi musamman a lokacin da na fara waƙa wannan ya sa sai na ji waƙoƙin suna yi mini daɗi sosai .

Mawaƙi yana alfahari da wata kyauta da aka yi masa. Ko kin taɓa samun wata kyauta ta girmamawa da aka yi miki?

E na samu kyautuka na kuɗi da yawa gaskiya kuma ina alfahari da hakan.

Bayan tarukan bikin Hausa da ake gayyatar ki, ana gayyatar ki wani taron?

Gaskiya na fi ga taron abubuwan da suka shafi al’adun gargajiya, sai kuma wani taron da aka gayyace ni na ƙaddamar da littafi kuma haka wasu wurare suke gayyata ta.

A wanne lokaci ne kika fi jin daɗin yin waƙa?

Ina jin daɗin rera waƙa ne idan Ina wani aiki ko gugar kayan makaranta, to na kan yi waƙoƙi saboda ina jin daɗin su sosai, ko kuma idan aka ɓata mini rai. To idan na yi waƙar sai na ji na dawo daidai.

Kowanne mawaki akwai abin da yake so ya cimma na buri a rayuwarsa. Ke wanne burin kike son ki cimma?

A gaskiya ina da burika da yawa , amma dai a yanzu matakin ma da nake ciki na ɗauki maganar waƙar ma na ajiye ta gefe ɗaya, na saka karatu a gaba, don haka duk da burin da nake da shi a tattare da waƙa, a yanzu karatu na saka a gaba.

To da yake ke ɗaliba ce, ko ya kike samun kanki a cikin ɗalibai ‘yan uwanki a matsayin ki ta mawaƙiya?

To da yake a makarantar mu yawanci ko suna da waya ko ta gidansu suna jin waƙoƙin da nake yi, idan suka ganni sai su rinƙa kira na Salma Sa’id, to a nan waɗanda ba su sanni ba ma sai suka sanni suka fara yi mini magana. Kuma wannan ya sa na yi kawaye sosai .

Ko akwai wata matsala da kike fuskanta a matsayin ki ta mawaƙiya?

E to ba na fuskantar wata matsala, duk da dai idan zan fita wani waje mahaifiyata za ta ce na rufe fuskanta don saboda mutane kamar idan zan je makaranta, domin duk wasu wurare ma sai da ita muke zuwa in ban da makaranta .

To wanne irin saƙo kike da shi ga masu sauraron waƙoƙinki musamman ganin a yanzu kin mayar da hankali wajen karatu?

To ina son su ci gaba da sauraron waƙoƙin gargajiya domin akwai fasaha da ilimi a cikin su, kada a tsaya ga jin waƙoƙin zamani waɗanda suka fi magana a kan soyayya wanda za ka ga abubuwan da ba na al’adun mu ba ake ɗakkowa ana sakawa, 

To madalla mun gode.

Ni ma nagode sosai.

By ukarofi