Ana kan tattaunawar dawo da Obi da Jonathan cikin PDP – Abba Moro 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sanata Abba Moro, wanda ke wakiltar Benue ta Kudu, ya bayyana cewa wasu mutane na tattaunawa da tsohon mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, da kuma tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan kan yiwuwar dawowarsu cikin jam’iyyar PDP.

Ya kuma yi nuni da cewa akwai yiwuwar Obi ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa na PDP a 2027 idan ya koma jam’iyyar.

Jaridar Manhaja ta rawaito cewa Moro ya bayyana haka ne a shirin ‘Politics Today’ na tashar Channels a ranar Talata.

Obi ya fice daga PDP domin tsayawa takara a jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023. A baya-bayan nan kuma, ya jingina da ƙawancen jam’iyyar ADC.

Jawabin Sanatan Benue ya zo ne a daidai lokacin da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yanke shawarar mika tikitin takarar shugaban ƙasa na 2027 ga yankin kudu.

Moro ya ce: “A matsayina na dan jam’iyya, PDP bata yi magana da Peter Obi ba tukuna. Amma a daidai wannan lokaci kafin 2027, ina sane da cewa wasu mutane na tattaunawa da shi domin a dawo da shi gida.”

Ya ƙara da cewa: “Ka dawo gida, ga abin da muke shirin yi. Idan ka dawo, kana da damar zama ɗan takara.”

Da aka tambaye shi ko tattaunawar za ta haifar da dawowar Obi cikin PDP, Moro ya ce babu wani abu tabbatacce a siyasa.

Moro, wanda ya amince da cewa yana cikin waɗanda ke tuntuɓar Obi, ya ce jam’iyyar za ta yi nazari sosai kan duk masu neman takara ciki har da gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, wanda shi ma yana sha’awar kujerar shugaban ƙasa.

By ukarofi