Yadda NNPC ya kashe biliyan N235.6 a wata bakwai wajen neman mai a Arewa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanin Fetur na Nijeriya (NNPC) ya cire zunzurutun kuɗi har Naira Biliyan 235.6 tsakanin watan Janairu zuwa Yulin 2025, don neman wuraren haƙo mai a arewacin Nijeriya, kamar yadda bayanan kuɗi na baya-bayan nan suka nuna.

Jaridar News Point Nigeria ta bayar da rahoton cewa, an cire kuɗaɗen ne a ƙarƙashin Asusun Harkokin Man Fetur (FEF) kamar yadda dokar masana’antar man fetur (PIA) ta tanada, a ɓangaren karen kashi 30 cikin 100 na kuɗaɗen da aka ware don gano wuraren da mai yake.

Wuraren da ake neman man sun haɗa da Basin Chadi, Tudun Binuwe, da filin Kolmani da ya ratsa jihohin Bauchi da Gombe.

Asusun, wanda aka tsara don karkata haƙar mai a Nijeriya daga yankin Neja-Delta, duk da haka ya haifar da zazzafar muhawara kan abubuwan ci gaban ƙasa.

Alƙaluman sun nuna irin kuɗaɗen da aka fitar na wata-wata:

Janairu: Dala miliyan 8.16m da biliyan N9.73 = biliyan N22.2

Fabrairu: Dala miliyan 17.59 da biliyan N5.8 = Biliyan N31.7

Maris: Dala miliyan 18.66 da biliyan N10.47 = Biliyan N38.3

Afrilu: Dala miliyan 28.51 da biliyan N17.71 = Biliyan N61.4 (mafi girma a lokacin)

Mayu: Dala miliyan 1.88 da biliyan N33.58 = Biliyan N36.5

Yuni: Dala miliyan 24.17 da biliyan N499 = Biliyan N38.7

Yuli: Dala miliyan 3.99 da Biliyan N732.9 = Biliyan N6.8

Jimlar Naira biliyan 235.6 na watanni bakwai ya nuna irin yadda gwamnatin tarayya ke tafiyar da aikin binciken wuraren haƙo a arewacin ƙasar, duk da mabambantan sakamakon da aka samu a shekarun da suka gabata.

A cikin watan Mayu, babban jami’in kamfanin na NNPC, Bayo Ojulari, ya sanar da cewa za a ci gaba da aikin haƙar mai a filin Kolmani, aikin da aka daɗe ana hasashe a tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.

Ojulari, wanda aka naɗa a watan Afrilu kuma fadar shugaban ƙasa ta yaba da shi a matsayin mai kawo sauyi, ya shaidawa Sashen Hausa na BBC cewa binciken mai arewacin ƙasar ya kasance babban fifiko a ƙarƙashin PIA.

“Gwamnati na kan hanyar samar da man fetur a Arewa,” inji Ojulari, yana mai jaddada kyakkyawan fata duk da shakku.

A cikin shekaru 20 da suka wuce, Nijeriya ta kashe sama da dala biliyan 3 wajen neman mai a arewacin ƙasar, ciki har da sanarwar da aka yi ta yada ganga biliyan daya a asusun ajiya, duk da cewa sakamakon hakoran da aka samu bai samu ba.

Girman rabon FEF ya sake haifar da damuwa game da daidaito tsakanin sabbin saka hannun jari da kuma al’ummomin yankin Neja Delta.

Bayanai daga Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NUPRC) sun nuna cewa a cikin shekaru huɗu, yankuna da ke haƙo mai sun samu jimillar Naira biliyan 328.2 ta asusun ci gaban al’umma (HCDF), inda biliyan N92.6 ne kawai fiye da kason da FEF ta ware a cikin watanni bakwai kacal.

By ukarofi