Daga UNCLE LARABI
“Mustapha manzona khatimul anbiya.” Wannan baitin amshin wata ƙasida ce da mu ke yi Lokacin Muna Yara a Makarantar Islamiyyarmu. Da yawan ’yan IzalaR yanzu duk mun yi Maulidi shekaru 30 da suka wuce.
Bayan Bikin Sallah Babba da Karama muna yara sai bikin Maulidi. Gaskiya an ci da rabon yaran yanzu. Idan watan Maulidi ya zo kusan kowanne gida sai an yanka kaji, wasu har raguna da shanu, ga soye-soyen su cincin da meat pie. Lokacin ba su pizza da doughnut. Sai dai su alkaki da dublan da algaragis da su bakilawa. Haka za a yi kunun zaki da zoɓo a ɗaura a leda ko lemon kwalba a yi ta bushasha a wajen Maulidi. A raba wa manyan baƙi da masu ziyara.
Yara mu yi ta karatun Maulidi. Ni kaina Uncle Larabi Ina cikin ɗalibai maza da suka fi kowa more hawa Gadon Aba’i, don Ina samun karatun Maulidi sama da kala 10.
1. Ina yin karatun Alƙur’ani Mai Girma. Ina karanta Izawaƙa’atul Waƙi’a ko Wannajamu Iza Hawa ko Waɗɗur ko Hami! Ina jin daɗin yadda nake rera karatun sosai, manya suna saurara, wani lokacin har kyauta nake samu ko kuma a yi ta son a gan ni, kamar wani ɗan fim a yanzu.
2. Ina karatun Isra’i da Mi’iraji. Ina karatanta Sama ta Huɗu. Na haddace ta sosai wallahi, amma yanzu karatun Sama ta Huɗu ya gudu wallahi. Sai abinda ba a rasa ba. Sama ta Huɗu nan ne inda ’yan Aljanna suke. Wani Lokacin Ina karatun Sama ta Biyar. A nan narkokin azaba suke. Ina tsorata sosai idan Ina karatun Sama ta Biyar duk da mata sun fi yawa a cikin wutar Jahanna. Bari ku ji wasu saɗara da na haddace har yanzu ban manta ba;
“Annabi Sallallahu Alaihi Wassalam ya ce, na ga wani mala’ika da zai kalli ƙasan duniya da duk sai ta narke. Duwarwatsu su fashe. Koguna su ƙafe.”
Akwai kuma Wajen da na sake riƙewa, inda ake cewa; “Annabi Sallallahu Alaihi Wassalam ya ce, na ga wasu mata bebaye kurame a cikin tanderun wutar Jahanna, wuta tana shiga ta ƙasansu tana fita ta samansu, naman jikinsu yana zagwanyewa, kamar kuturta-kuturta. Sai ya tambayi Mala’ika Jibrilu (AS) waɗannan su wane ne? Sai Mala’ika Jibrilu ya ce, waɗannan sune masu ha’intar mazajensu.
Akwai wani wajen ma da ake cewa, na ga wasu mata ana yi musu azaba suna kira suna kuka a cikin tanderun wutar Jahanna. Sai na tambayi Mala’ika Jibrilu (AS) waɗannan su wane ne sai ya ce, waɗannan sune masu cewa da mazajensu, mamakin abin da ya munana lamarinka, ko warinsa ma ba na so na Ji, ka sake ni, ba tare da wani uzuri ba, saboda tsananin sababi da sauransu dai.
3. Ina karatun Siratunnabiy Sallallahu Alaihi Wassalam. Yawanci na fi karanta Nasabasar Sallallahu Alaihi Wassalam ko darasi na Tara; Aiko Annabi Sallallahu Alaihi Wassalam.
4. Ina karatun Hayatul Islam, wanda ake cewa, su sa’ali tambaya, ja jawabi.
5. Ina karatun Ahlari, Ina karanta Babul Mujibatul Ghusuli, babin masu wajabta wanka. Lokacin Ina jin tsananin kunya idan Ina karatun wannan babin.
6. Ina karanta Arba’una Hadith. Ina cikin yaran farko a faɗin Kano da suka fara karatun Arba’una Hadith da Turanci. Ba na mantawa har kyaututtuka na samu. Farko na karanta Hadith na 16 ne da Larabci, na karanta da Hausa, fassara kenan, sannan na yi ‘translation’ da Turanci. Na san akwai yara ’yan bana-bakwai da za su iya ƙaryata ni to da yawa ba a haifi wasu ba ma a masu karatun yanzu, don na karanta ne a 1994-1995. Na Karanta Hadith ɗin da yake magana akan girmama baƙo da girmama maƙoci da kuma ka yi magana mai kyau ko ka yi shiru. Ga Kaɗan daga cikin fassarar da na yi a wancan Lokacin;
“Whose ever believe in Allah and the last day (that’s the day of Judgement) speak good or be silent. Whose ever believe in Allah and the last day, respect your neighbor. Whose ever believe in Allah and the last day, honor his guest.”
Lokacin kun ji kabbara da zuwa ana gaisawa da ni? ɗan ƙaramin yaro ya yi karatu da harshe uku? Larabci, Hausa, Turanci! Masha Allah!
7. Ina karatun Hadith na Maj’mu’ul Bahrain.
Akwai wasu littattafan da nake karantawa ranar Maulidi, wallahi na manta, don na san Ina karatu fiye da 10. Duk sanda za a juya idan aka ce za mu koma kan karatun littafin kaza, to za a kira sunana. A waje biyu ne bana hawa ‘role’ ɗin shine wajen ƙasida da kuma wajen wasan ƙwaiƙwayo da ake yi, don faɗakarwa a Islamiyya a wajen Maulidi. Alhamdulillah.
Yaran yanzu da yawa ba su more wannan ba. Ko a yanzu inda suke Maulidi ba kowa ke da damar yin klaratun kamar haka ba. Sannan a wancan lokacin tun bayan sallar Isha ake fara Maulidi har wayewar gari, wani lokacin zuwa ƙarfe 7:00 ko 8:00 na safe. Ya danganta da juyawar yanayi; sanyi ko zafi ko damina. Sannan ana yi mana alibidi; shinkafa da miya ko da taliya ko makaroni da naman kaji ko naman kasuwa (naman rago ko akuya da sauransu). Wani lokacin har doya ma ana ɗan yayyanka mana. Amma ba a yi da salak a lokacin, sai ɗan kunun zaƙi ko lamurje kpo lemon kwalbar da mutum zai sha.
Allah mun gode maka bisa baiwarka da ni’imarka da ka yi mana.
Allah ya ƙara wa Manzo Sallallahu Alaihi Wassalam wasila da fadila. Allah ya ƙara mana so da ƙaunar Manzo Sallallahu Alaihi Wassalam. Barka da shigo wa watan Maulidi na shekarar 2025.
Abdullahi Jibril Dankantoma (Uncle Larabi), Jihar Kano, Nijeriya, 08065418892
Litinin, 25 ga Agusta, 2025
