
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin jihar Sokoto ta ce da yanzu za ta riƙa biyan alawus a kowane wata ga limamai, mataimakansu da ladanai a dukkan masallatai, tare da ƙara tallafi ga masallatan Juma’a a jihar.
Gwamna Ahmed Aliyu ya sanar da haka a ranar Asabar yayin taron yaye mahaddata guda 111 daga makarantar Gidauniyar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi a jihar.
Ya ce, sabon tsarin bada alawus ɗin an samar da shi ne da nufin ƙarfafa wa limamai da ladanai wajen sauke nauyinsu cikin inganci da tabbatar da karantarwa addinin Musulunci ya cigaba a jihar.
Ya bayyana cewa, za a riƙa biyan masallatan Juma’a daga N300,000 zuwa N500,000 dogaro da matakinsu.
Haka kuma limamai da ladanai da mataimakansu za su riƙa samun alawus a kowane wata domin ƙarfafa wa hidimar da suke yi wa addini.
Haka kuma, gwamnatin ta ce karin kudaden da aka ware ga masallatan Juma’a za su taimaka wajen gudanar da ayyukan yau da kullum, kula da masallatai da kuma samar da tsabtar muhalli ga jama’a.
Wasu jama’a da suka zanta da manema labarai sun bayyana cewa wannan mataki ya nuna yadda gwamnatin jihar ke mutunta addini da shugabannin addini tare da jaddada muhimmancin hadin kan al’umma.
Masana harkokin al’umma sun bayyana wannan tsari a matsayin babban ci-gaba wajen inganta zaman lafiya da kuma bunkasa hadin kan jama’a a jihar.
