Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A ƙoƙarin samar da zaman lafiya mai ɗorewa, a Jihar Katsina, ƙaramar hukumar Musawa tayi zaman sasanci da ‘yan bindiga a yankin.
Shugaban ƙaramar hukumar Musawa Hon. Aliyu Idris Gingin, Sarkin Musawan Hakimin Musawa Alhaji Sagir Inde, da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Musawa Hon. Lawal H. Yaro Away, da Alhaji Bala Abubakar Musawa da sauran shugabannin na ƙaramar hukumar Musawa suka jagoranci sasanci
Su ka jagoranci sasanci da yan bindigar a dajin Tashar Mai Alewa dake cikin ƙaramar hukumar Ɗanmusa.
Daga ɓangaren ‘yan
bindigan akwai Mannore, Kamilu Buzare, da Wada Yalo wanda shi ɗan asalin ƙaramar hukumar Musawa ne.
Ɗaya daga cikin shugabannin ƴan bindigar Mannore ya yaba da yadda zaman sasancin ya wakana,ya ba al’ummar ƙaramar hukumar Musawa tabbacin amincewa da zaman lafiya tare da daina kai hare, hare da satar mutane a ƙaramar hukumar Musawa.
Ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar Musawa, mataimakin shugaban jam’iyyar APC ta Jihar Katsina Alhaji Bala Abubakar Musawa a nasa jawabi ya bayyana gamsuwar shi, akan yadda Fulanin su ka rungumi zaman lafiya a yankin ƙaramar hukumar Musawa.
Ya ce bayanai da shugabannin Fulanin suka gabatar, a matsayin abun dubawa ne da nazari akai domin ɗorewar zaman lafiyar a yankin.
A nashi jawabin, Sarkin Musawan Katsina, Hakimin Musawa Alhaji Sagir Inde ya nuna jin daɗin shi, akan wannan yarjejeniyar zaman lafiya da akayi a yankin ƙaramar hukumar.
Sai ya bayyana akwai kyakkyawar dangantaka da zumunci dake tsakanin Fulani da Hausawa, “Amma kwatsam wasu dalilai su ka sa dangantaka yayi rauni.
Sarkin Musawa ya yi fatan maido wannan dangantaka kamar yadda take a tsakanin, Fulani da Hausawa na zumunci da ƙaunar juna.
Game da buƙatar Fulanin na samar masu da burtali domin samar da wuraren kiwon dabbobinsu, Hakimin ya yi alƙawarin bin kowace mazaɓa ta yankin Gundumar Musawa domin fidda masu burtullan.
Daga ƙarshe shugaban ƙaramar hukumar Hon. Aliyu Idris ya bayyana farin cikinsa da Allah ya nuna masa wannan rana mai matuƙar mahimmanci ta yin yarjejeniyar zaman lafiya a ƙaramar hukumar Musawa,ya kuma yi alƙawarin aiwatar da buƙatun da su ka gabatar a lokacin zaman sasancin domin ɗorewar zaman lafiya a yankin.
Taron ya samu halartar ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Musawa Hon. Lawal H. Yaro Away, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Musawa da Matazu Hon. Abdullahi Aliyu Dujiman Katsina wanda ya samu wakilcin Hon. Isma’il Kira mai taimaka ma ɗan majalisar akan ayyukan mazaɓa. Da dai sauransu.
Ya zuwa yanzu ƙananan hukumomi 6 kenan su kayi sasanci da ‘yan bindiga a yankunan su.
Sun haɗa da ƙananan hukumomin Jibiya, Batsari, Safana, Danmusa, kurfi da Musawa .
