
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Sufuri, Sa’idu Ahmed Alƙali ya tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa nan ba da jimawa ba za a gyara wuraren da suka lalace na layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna a makon da ya gabata.
Lamarin ya auku ne sakamakon gocewa da wani jirgin ƙasa da ya yi jigilar mutane daga Abuja ya yi, inda ya nufi Kaduna a ranar Talata.
Duk da cewa da dama daga cikin fasinjojin sun tsira, guda bakwai daga ciki sun samu raunuka, inda aka garzaya da su asibiti jim-kaɗan bayan faruwar al’amarin.
Da yake jawabi a wajen da abin ya faru a ranar Litinin, Minista Alƙali ya yaba wa hukumomin tsaro da suka kai ɗauki wajen tare da bada kariya ga al’ummar da abin ya shafa.
Ya kuma ce, nan da kwanaki goma za a kammala gyaran sashin da suka lalace sakamakon aukuwar lamarin.
A ƴan shekarun nan layin dogo na Abuja zuwa Kaduna, wanda dubunnan mutane suke amfani da shi, ya samu ƙalubale ta fuskar tsaro da gudanarwar.
