
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar Sojojin Nijeriya ta nesanta kanta daga zargin cewa tana bai wa ƴan bindiga kuɗaɗe, lamarin da ta ƙaryata da babbar murya inda ta ce ba ya daga cikin salonta biyan kuɗin fansa ko alawus gare su a kowane wata wajen daƙile ayyukan ta’addanci.
Shugaban tsaro na gudanarwa, Manjo Janar Emeka Onumajuru ya faɗi haka a yau Talata yayin hira da gidan talabijin na Channels.
Ya bayyana cewa, biyan kuɗaɗe ga ƙungiyoyin ƴan ta’adda abu ne da ke ƙara musu karfi a madadin daƙile ayyukansu na ta’addanci.
Ya kuma ce, a madadin haka rundunar sojoji tana aiki tuƙuru wajen katse hanyoyin samar musu da makamai da watsa su a ƙarƙashin shirin gyaran hali na DDR da haɗin-gwiwar Ma’aikatar Shari’a da ofishin mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro.
Shirin DDR yana aiki ne a ƙarƙashin atisayen Safe Corridor a jihohin Gombe da Zamfara da nufin gyaran hali ga tubabbun mayaƙan ƴan ta’adda da waɗanda suka miƙa makamai.
Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya yi zargin cewa Gwamnatin Tarayya tana biyan ƴan ta’adda kuɗaɗen alawus da aika musu abinci da sunan hanyar daƙile ayyukansu.
