Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban ƙungiyar ‘yan ƙwadago, watau NLC, reshen Jihar Katsina, Alhaji Hussaini Hamisu ‘Yanduna, ya buƙaci gwamnatin Jihar Katsina da ta ƙara yawan kayan abincin da take samarwa a shagunanta na Rumbun Sauki.
Da yake zantawa da jaridar Manhaja a Katsina, Alhaji Hussaini ‘Yanduna ya lura cewa a halin yanzu taliya da shinkafa ne kadai ake samarwa a shagunan Rumbun Sauki guda uku dake Katsina.
Ya buƙaci gwamnati ta riƙa sayar da sauran kayan abinci da ake amfani da su yau da kullum, kamar masara, da gero, da wake, da fulawa, da suga, da man-gyada.
Amma shugaban na NLC ya yaba ma gwamnatin Jihar Katsina bisa kirkirar shirin, wanda yace ya kawo sauƙi ga ma’aikata a jihar ta hanyar rage yawan kuɗin da suke kashewa wajen sayen kayan abinci.
Game da shirin inshoran kiwon lafiya na ma’aikata a jihar, shugaban ƙungiyar ma’aikatan ya bayyana takaicin yadda ma’aikata basa samun cikakken biyan buƙatar daga shirin.
Alal misali, yace a duk lokacin da ma’aikaci ko wani makusancinsa ya je asibitin da lalurar rashin lafiya da yamma, sai a ce masa sashen inshoran kiwon lafiya na asibitin sun tashi daga aiki, ya dawo da safe.
Don haka ya shawarci gwamnatin jihar Katsina da ta ja kunnen asibitocin da ke ƙarƙashin wannan shiri na lafiya.
Ko da yake Alhaji Hussaini ‘Yanduna ya yaba ma gwamnatin jihar bisa ƙirƙiro shirin, wanda yace ya kawo rangwame ga ma’aikata musamman wajen kashe kuɗi a kan neman lafiya.
Har ila yau shugaban na ƙungiyar NLC wanda kwanakin baya masarautar Daura ta naɗa shi sarautar Sarkin Gabas, ya bayyana wasu nasarori da ƙungiyar ƙwadago ta samu a ƙarƙashin jagorancinsa, da suka haɗa da ƙarin albashi har karo biyu ga ma’aikata.
Ya ce a karon farkon, an ƙara wa ma’aikata albashi zuwa N30,000, a karo na biyu kuma aka kara musu albashin ya kai N70,000 wanda aka fara biya nan take.
Alhaji Hussaini Hamisu ‘Yanduna yace an kuma samu nasarar basu damar kai wa matakin aiki na GL16, watau matakin Darakta.
