Yanzu-yanzu: Tinubu ya tafi hutun shekara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya tafi Turai daga Abuja domin fara hutunsa na shekarar 2025, kamar yadda Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana.

A wata sanarwa ta hannun Kakakinsa Bayo Onanuga, hutun Shugaban ƙasar zai fara ne daga yau 4 ga watan Satumba, wanda kuma zai shafe tsawon kwanaki 10.

Tinubu zai yi hutun nasa ne a tsakanin ƙasashen Faransa da Birtaniya, inda zai dawo gida Nijeriya bayan haka.

Duk da cewa hakan hutu ne a gare shi, zai kuma yi amfani da damar wajen halartar tarukan da suka shafi shugabanci idan buƙatar hakan ta taso.

By Babaji