Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana haka a lokacin da yake ƙaddamar da gudanar da addu’o’i na musamman don neman taimakon Allah wajen shawo kan matsalar tsaron da ta addabi jihar.
Taron ya haɗa shugabannin addini, dattawa da jami’an gwamnati, inda aka yi addu’o’i tare da ƙara neman haɗin kai wajen fuskantar matsalar tsaron da jihar ke fama da ita.
Da yake buɗe taron Gwamna Dikko Raɗɗa ya fara da addu’o’i na musamman ga waɗan da suka rasa rayukan su sakamakon matsalar tsaro da kuma samun waraka ga waɗanda suka jikkata.
Ya jaddada cewa matsalar tsaro ba ta banbance ƙabila, addini ko jam’iyya ba, don haka matsala ce da ke buƙatar haɗin kai, haƙuri wajen shawo kanta.
“Ƴan ta’adda ba sa tambayar ko kai dan APC, PDP, ADC, ko kuma wata jam’iyyar daban, Saboda haka wajibi ne mu zama al’umma guda, rigingimu ba za su iya magance abin da haɗin kai da kuma fahimtar juna basu magance ba” Inji Gwamna Raɗɗa.
Gwamnan kuma ya bayyana wasu matakan da gwamnatin sa ta ɗauka, ciki har da ɗaukar matasa jami’an C-watch daga yankunan da abin ya fi shafa domin tallafa wa Sojoji, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro.
Ya ce gwamnatin jihar ta ƙaddamar da sabbin motoci masu sulke guda takwas da sayen babura guda 700 domin ƙara taimakawa wajen shawo kan matsalar musamman a wuraren da ke da wahalar shiga.
Haka kuma, Gwamnan ya bayyana ƙoƙarin da gwamnatin sa ke yi idan aka samu rahoton hare hare na ƴan bindiga , nan take muke tallafawa iyalin waɗanda suka rasa rayukansu,idan kuma rauni ne gwamnatin Katsina ce ke ɗaukar nauyin maganin su,”Dikko ya ce.
Ya ja hankalin al’umma kan lalacewar tarbiyya, inda ya roƙi iyaye, malamai da shugabannin al’umma da su ci gaba da kula da tarbiyyar yara.
“Wallahi ba don a sake zaɓe na nake ƙoƙarin magance matsalar tsaro ba. A’a. Ina yin bakin ƙoƙari na ne saboda sauke nauyin da Allah ya ɗora a kaina, na kare rayuka da dukiyar al’umma. Kuma Allah ne shaida,”inji malam Dikko
A jawabin sa Mataimakin Gwamna Malam Faruk Lawal Joɓe, ya jaddada muhimmancin addu’a wajen samun zaman lafiya, tare da yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa bisa irin ƙoƙarin da yake yi wajen shawo kan matsalar tsaro ta hanyar farfaɗo da noma da kiwo wanda suka durƙushe sakamakon matsalar tsaro.
Ya bayyana yadda gwamnati ta raba takin zamani, abinci a lokacin azumin watan Ramadan, tare da wani shiri na karyar da farashin kayan abinci domin rage wa mutane raɗaɗi.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasiru Yahaya Daura, ya yabawa al’ummar Katsina bisa addu’o’i da goyon baya da suke ma wannan gwamnati. Ya kuma yaba ma irin gudunmawar da malamai, da dattawa ke bayarwa wajen ci gaba da addu’o’i domin neman zaman lafiya.
Ya buƙaci shugabanni da al’umma da su haɗa kai tare da ƙara jin tsoron Allah, gaskiya, haƙuri, tausayi da bayar da zakka a matsayin halayen da za su taimaka wajen shawo kan matsalar. Ya kuma yaba ma ƙoƙari da jajircewar Gwamna Raɗɗa wajen dawo da zaman lafiya a Jihar Katsina.
A nasa jawabin Kwamishinan harkokin addini, Alhaji Ishaq Shehu Dabai, ya bayyana cewa an shirya gudanar da taron addu’o’in ne na musamman don neman yardar Allah a kan matsalar tsaron da ta addabi jihar.
Manyan malaman Izala da na ɗariƙa duk sun gudanar da addu’o’i a wajen taron.
