A ranar 3 ga Satumba 2025, kamfanin kayan kwalliya na duniya, Lush, ya ɗauki matakin da ya jawo cece-kuce, ya rufe dukan shagunan sa a Scotland da fiye da ɗari a duk faɗin Birtaniya na tsawon yini ɗaya.
A ƙofar shagunan, an rataya allon da ke ɗauke da rubutu: “STOP STARVING GAZA – WE ARE CLOSED IN SOLIDARITY”, wato “Ku dakatar da azabtar da Gaza – mun rufe don nuna goyon baya.” Hakan ya zama alamar tsayuwa da Gaza a lokacin da dubban jama’a ke mutuwa daga yunwa da hare-hare.
Kakakin kamfanin ya bayyana cewa: “Ba za mu iya ci gaba da gudanar da kasuwanci tamkar babu abin da ke faruwa ba, yayin da miliyoyin yara da mata ke mutuwa daga yunwa a Gaza. Wannan rufewa na yini ɗaya wata hanya ce ta tayar da hankali a duniya.”
Matakin ya jawo martani iri-iri. Wasu sun yaba wa kamfanin saboda nuna adalci da tausayi, suna cewa hakan zai iya ƙara matsa lamba ga gwamnatocin yamma. Amma wasu ‘yan siyasa sun soki matakin, suna cewa kamfanoni ba su da hurumin shiga rikicin siyasa ta wannan hanya.
Masana tattalin arziki sun ce wannan mataki ba wai kawai ya nuna kishin ɗan adam ba ne, har ma ya zama alamar yadda kamfanoni ke iya shiga cikin dabarun siyasa ta hanyar kasuwanci. An kuma lura cewa bayan wannan mataki, dubban jama’a a shafukan sada zumunta sun yaba da Lush, abin da zai iya ƙara masa kwarjini a kasuwa, duk da yiwuwar fuskantar cikas daga masu adawa.
