
Sifeton rundunar ƴan sandan, Kayode egbetokun ya naɗa CSP Benjamin Hundeyin a matsayin sabon mai magana da yawun rundunar ƴan sanda a mataki na ƙasa (FPRO)
Naɗin Hundeyin na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar mai barin gado, Muyiwa Adejobi ya fitar.
”Babban Sifeton ƴan sandan ya buƙace shi da aiki da ƙwarewarsa ta sadarwa wajen inganta aikin ɗan sanda a Nijeriya ta hanyar ƙarfafa hulɗa da jama’a,” inji sanarwar.
Kafin sabon muƙamin, CSP Benjamin Hundeyin ya kasance kakain rundunar ƴan sanda reshen jihar Legas, inda ya kwashe shekaru yana aiki a matsayin.
