Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Nijeriya, Hadi Sirika, ya musanta zargin cewa aikin samar da kamfanin jirgin saman Nijeriya na ‘Nigeria Air’ da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ta ƙaddamar a zamaninta ba na bogi ba ne.
Sirika, wanda ya riƙe muƙamin minista sau biyu, ya bayyana hakan ne ga gidan talabijin na Channels a ranar Talata inda ya ce an bi dukkan ƙa’idoji.
Ya ƙara da cewa aikin samar da jirgin saman haɗin gwiwa ne tsakanin gwamnati da masu zaman kansu, ƙarƙashin kulawar hukumar tafiyar da haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu.
Tsohon ministan ya musanta batun cewa ya kashe naira biliyan 100 wajen aikin inda ya ce jimillar kuɗin da aka yi kasafi domin aikin samar da kamfanin sufurin shi ne naira biliyan 5 inda aka saki naira biliyan 3 kuma ya bar fiye da biliyan ɗaya lokacin da ya sauka daga muƙaminsa.
An ƙaddamar da Nigeria Air a ƙarshen mulkin Buhari, duk da cewa wasu sun ce aikin na bogi ne da kuma zamba.
Tun bayan ƙarewar wa’adinsa na minista a 2023, Sirika ya riƙa fuskantar shari’a kan zargin almundahana da amfani da muƙaminsa ba bisa ƙa’ida ba.
Hukumar EFCC ta zarge shi da bai wa kamfanonin ‘yan uwansa, ciki har da ‘yarsa kwangiloli da suka kai na biliyoyin naira.
