Nijeriya za ta sayar da matatun mai huɗu da filayen jirgin sama biyar ga ‘yan kasuwa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Najeriya ta bayyana shirin sayarwa ko kuma miƙa wa ‘yan kasuwa ragamar gudanar da kamfanonin ƙasar aƙalla 91 na wani wa’adi, ciki har da kamfanin samar da ƙarafa na Ajaokuta, da matatun man fetur huɗu da kuma manyan filayen jiragen sama guda biyar.

Yayin ƙarin bayani a kan shirin, shugaban hukumar kula da hada-hadar sayar da kadarorin gwamnatin Nijeriya, Mista Ayodeji Ariyo, ya ce za a aiwatar da matakin ne domin farfaɗo da kamfanonin daga durƙushewar da suke fuskanta sai kuma jan ra’ayin hamshaƙan masu zuba jari, dama samar da kuɗaɗen shiga ga gwamnati.

Kamfanoni ko wuraren da wannan ciniki zai shafa akwai kamfanin ƙarafa na Ajaokuta, dandalin Tafawa ɓalewa da aka fi sani da TBS kana, Kasuwar Bajekoli da ke jihar Legas sannan matatun man ƙasar guda 4 da kuma tashoshin jiragen sama guda 5.

A cewar Mista Ayodeji Ariyo Gbeleyi, yayin jawabinsa na jiya Talata a Abuja, za a gudanar da wannan cikini a fayyace kuma bisa tanadin doka ba tare da barin komai a duhu ba, ta hanyar shiho da dukkanin fannonin ƙwararru ta fuskar kuɗi da kuma shari’a.

Cikin jawabin nasa, Mista Gbeleyi ya ce akwai alkhairi a wannan tsari na jinginarwa ko kuma miƙa kadarorin gwamnatin ga ‘yan kasuwa, inda ya gwada misali da lokacin da aka miƙa ragamar kamfanonin sadarwa da harkokin fansho dama hada-hadar tashoshin jiragen ruwa baya ga harkar sufurin jiragen sama hannun ‘yan kasuwa, wanda ya taimaka matuƙa ta hanyar ɗorewar ayyukansu dama samar da kuɗin da ya haura dala biliyan 2 da rabi.

By ukarofi