Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Unguwanni da suka haɗa da Layi quaters,Kofar Yamma, Gyara, Unguwar Rini,Bakin Kasuwa da wani ɓangare na Sabon Birnin kusan duka ruwan sama ya shafe.
Unguwanni Kamar su Sabuwar Abuja Kanti da Ghaci wasu daga cikin gine gine-ginen su ya rufa.
Haka ya sanya dubban mutane suka rasa matsuguni wanda ya kai su raɓuwa a maƙwabta, wasu kuma wajen yan uwansu.
Mafi yawa mutanen da iftala’in ya rutsa da su ,suna nuna kaɗuwa da damuwa inda suka ce wannan bala’i shine na farko da ya taɓa faruwa bayan shekara arba’in da suka wuce.
Wani magidanci Shehu Mustapha ya shaidawa manema labarai da suka je gani da ido cewa bayyana cewa gidan sa dana makwabtakan sa a unguwar Sabon Birni suka sun ruguje sakamakon wannan ambaliyar.
Ya alaƙanta lamarin da lalacewar wata madatsar ruwa na garin kankia.
Mustapha ya ce wannan madatsar ruwa na neman gyara gaba ɗaya domin a cewar sa ba zai iya riƙe ruwa ba.
“Madatsar ruwan ba zata iya tare ruwan ba duka saboda yana zuwa da ƙarfi,”inji magidanci.
Shima Abubakar Abdullahi wanda ya rasa gidansa da dukiyar da ya bayyana cewa yawancin al’ummar yankin basu taɓa gani ruwan sama mai yawa irin na daminar bana ba.
Ya danganta afkuwar ambaliyar ruwan da rashin kwashe shara a magudanan ruwa da wasu hanyoyin wucewar ruwa.
Magidancin ya bayyana cewa bayan rushewar gidaje ruwan kuma ya lalata gonaki da dama a yankin.
Shugaban ƙaramar hukumar ta kankiya Alhaji Lawal Abdullahi ya bayyana wa manema labarai cewa ya zagaya wuraren da ambaliyar ruwan ya yi ɓarna domin gane ma idanunsa.
Ya ce ba zai iya bada adadin yawan gidaje da suka ruguje ba domin akwai yiwuwa wasu ƙarin gidaje su faɗi.
Shugaban ƙaramar hukumar ya sanar da cewa yanzu haka yana tare da jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa SEMA suna zagayawa wanda daga baya zai yi cikakken bayani.
“Tunda aka haife ni ban taɓa ganin irin wannan iftala’i ba ,na shiga ƙauyen Tafashiya na yadda ruwan sama ya kusan shafe kauyen,”inji Alhaji Lawal.
Sai da ya danganta lamarin daga Allah,yayi addu’a Allah ya kare afkuwar haka nan gaba.
