Kisan jaruma Laila Khan da iyalinta ya shiga tarihi a kotun Mumbai

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Al’umma sun sake tunawa da Laila Khan, wacce ta fito a fim ɗin Wafa: A Deadly Loɓe Story tare da Rajesh Khanna a shekarar 2008. Laila da iyalinta guda biyar sun gamu da ajalinsu a shekara ta 2011, a wani kisan gilla da ya girgiza Bollywood.

A wannan mako, kotun Mumbai ta bayyana cewa, wannan kisan ya zama abin ban mataki wajen irin mummunan laifi, inda alƙalin ya bayyana shi a matsayin “rarest of rare”. Wannan kalma na nufin cewa laifin ya sha bamban ko in ce ya zama ɗaya cikin dubu na yadda aka saba gani a kundin laifuffukan Indiya.

Bayan wannan hukunci, masu rajin kare haƙƙin mata sun buƙaci gwamnati ta ƙarfafa matakan tsaro ga jarumai mata. Haka kuma, masana harkar fina-finai sun yi kira da a samar da tsare-tsare na musamman domin tabbatar da amincin ’yan fim da iyalansu.

By ukarofi