
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kimamin mutane takwas suka rasu yayin da sama da guda 20 suka jikkata a lokacin da ƴan bindiga suka farmaki al’umma a ƙauyukan Wakeh da Gadaneji da ke Gundumar Agunu a Ƙaramar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna.
An ruwaito cewa maharan sun kuma yi garkuwa da wasu da ba a san adadinsu ba a yayin farmakin, wanda suka ƙaddamar a sanyin safiya, kamar yadda mazauna yankunan suka shaida wa manema labarai.
Mai sharhi akan lamuran tsaro, Zagazola Makama a wani rubutu ta kafar X, ya ce maharan sun kai mummunan hari ne a yankin Wakeh inda suka kashe mutane masu yawa da raunata wasu da dama waɗanda wasunsu ke cikin mawuyacin hali.
Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaye sunansa ya tabbatar wa Blueprint faruwar al’amarin, saidai bai bada ƙarin bayani a kai ba.
Hakan kuma ba a yi nasara ba wajen ji ta bakin Shugaban Ƙaramar Hukumar, Hon. Manzo Daniel Maigaru, amma a wani saƙo daga mataimakinsa na yaɗa labarai, Daniel Gideon a Facebook, ya ce Ciyaman ɗin ya kai ziyara ga mutanen da iftila’in ya rutsa da a Asibitin St. Gerard da ke Kaduna tare da mataimakinsa Hon. Hussaini Abdullahi da kuma ɗan majalisar yankin Majalisar Dokokin jihar, Rt. Hon. Peter Agite.
