
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya sanar da dakatar da gajeren hutun da ya tafi na kiwon lafiya, bayan fama da wani rashin lafiya.
A saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon gwamnan na Anambra ya bayyana cewa ya shiga hailn rashin lafiya ne a lokacin da ya je halartar wani taro a Jihar Inugu a ranar Juma’ar da ta gabata.
A bisa shawarar likitocinsa ne ya dakatar da baki ɗaya hada-hada a bainar jama’a a ciki da wajen Nijeriya.
Bayan dawowarsa daga hutun ne a ranar Litinin, Obi ya ce ya ziyarci wajen kasuwancin wata ƙaramar ƴar kasuwa da ke aikin ɗinki da ma’aikatanta bayan haɗuwarsa da ita yayin ziyarce-ziyarcensa.
A nan ne ya ƙara musu ƙwarin-gwiwa ganin yadda suke aiki tuƙuru wajen samar abubuwa daban-daban, inda ya ce samarwa abu ne da ke taimaka wa lamuran ci-gaba a ƙasa, yana mai bada misali da ƙasar Bangladesh inda harkar yadi ke samar Dala biliyan 50 a kowace shekara.
A ƙarshe, ya yi godiya ga ɗaukacin al’ummar da suka yi ta masa addu’o’in samun waraka daga rashin lafiyar da ta same shi.
