Fasto Jerry ya sake zama ɗan Nijeriya mafi samun kuɗi a YouTube

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Fasto Jerry Eze, wanda shi ne ya samar da ‘Streams of Joy International’, ya sake zama ɗan Nijeriya mafi samun kuɗin a kafar YouTube a karo na biyu.

A jaddawalin waɗanda suka fi samun kuɗin shiga da fage sharhi akan harkokin YouTube, wato Playboard ya fitar, faston shi ne wanda aka fi kallon tasharsa a ƙasar inda aƙalla kimanin mutane 282,451 ke kallo.

Tashar, wadda ke da alaƙa ta kai-tsaye da Streams of Joy, a yanzu tana da mabiya miliyan 2.87 da kuma bidiyoyi sama da guda 2,900.

Aƙalla mutane miliyan 80 ne suka kalli bidiyoyinsa a shekarar 2025, lamarin da ya sa Playboard ta yi jimillar abinda ya ke samu a kowace rana a matsayin Naira miliyan 1.94.

Rahoton ya kuma nuna cewa waɗanda suke bin Eze a baya sune Paul S. Joshua na Cocin The Refiner’s House Ministries da Dunamis TV ƙarƙashin jagorancin Fasto Paul Enenche na Dunamis International Gospel Centre, sai wanda ya samar da Celebration TV, wato Apostle Johnson Suleman na Omega Fire Ministries, da kuma Rev. Sam Oye na The Transforming Church.

Sauran tashoshin Nijeriya masu tara maƙudan kuɗaɗe a kafar sune Babylon, UKFamilyShow, Eno Jerry, Catholic Reflection Family, Johnson Suleman, Harvesters TV, Free Indeed TV Ministry, Berekete Family da kuma Fada Ebube Muonso.

By Babaji