Ghana ta amince da karɓar ƴan Yammacin Afirka da Amurka ta koro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ghana ta zama ƙasar da a ƴan kwanakin nan ta karɓi mutanen da Amurka ta koro su a ƙarƙashin shirinta na koro baƙin haure da ke zama a ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.

Shugaba John Mahama na Ghana ya ce yanzu za su riƙa karɓar ƴan Afirka ta Yamma a cikin ƙasarsa, wanda hakan wani ɓangare ne na yarjejeniyar da ke tsakaninsu da Amurka. Tuni guda goma sha huɗu suka sauka a Ghana daga Amurka.

Ya kuma kafa hujja da dokar ECOWAS ta ba ƴan ƙasashen ƙungiyar damar zama a ƙasashen shiyyar da ba nasu ba ba tare da biza ba.

A watan da ya gabata ne Amurka ta koro baƙin haure bakwai zuwa ƙasar Ruwanda, yayin da a watannin baya aka tura biyar zuwa Eswatini da wasu takwas zuwa Sudan ta Kudu.

Shugaba Mahama ya kuma ce galibin mutane 14n ƴan Nijeriya ne da wani ɗan Gambiya ɗaya.

Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta nemi ƙasashen Afirka da dama da su bai wa mutanen da ta kora mafaka a ƙoƙarin Amurka na sanya takunkumin shige da fice, lamarin da wasu ƙasashe suka ƙi amincewa da shi ciki har da Nijeriya duba da yadda ake koro waɗanda wasun su fursunoni ne daga wasu ƙasashe.

By Babaji