
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Alhamis Majalisar Dokoki ta Jihar Benuwai ta rushe tawagar jagororinta, inda ta bar kaɗai Kakakinta, Alfred Emberga da Mataimakinsa, Lamin Danladi.
An ɗauki matakin ne yayin zaman majalisar na ranar bayan miƙa ƙudirin hakan daga tsohon mataimakin jagoran mafi rinjaye na majalisar, wato Douglas Akya.
Akya ya ce, tunda ƙaramar hukumarsu ɗaya da na Kakakin, kuskure ne a ce ya cigaba da zama a matsayin mataimakin jagoran mafi rinjaye.
Bayan miƙa ƙudirin ga fagen zaɓe, mambobin majalisar suka amince da shi.
Daga nan aka naɗa muƙaman ga Pharm. Thomas Dugeri (APC/Kwande West) a matsayin jagoran mafi rinjaye; Dakta Abraham Jabi (APC/Buruku) a mataimakin jagoran mafi rinjaye; Mista Cyril Ikong (APC/Oju) mai tsawatarwa na mafi rinjaye; da kuma Mista Simon Gabo (APC/Mata) a matsayin mataimakin mai tsawatarwa.
Sauran sun haɗa da Mista Abu Umoru (PDP/Apa) a matsayin jagoran marasa rinjaye; Mista Cephas Dyako (LP/Konshisha) a matsayin mataimakin jagoran marasa rinjaye; sai Mista Samuel Jiji (PDP/Logo) a mai tsawatarwa naarasa rinjaye; da kuma Mista Moses Egbodo (PDP/Obi) a mataimakin mai tsawatarwa na marasa rinjaye.
