Hukumar NOA a Tarauni ta wayar da kan jama’a kan muhimman batutuwan ƙasa

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Ofishin Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta ƙasa (NOA) a ƙaramar Hukumar Tarauni, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Shamsiyya Ibrahim, ta ƙaddamar da gagarumin wayar da kan al’umma domin magance muhimman matsalolin ƙasa a matakin ƙaramar hukumar.

A cewar jami’in yaɗa Labarai na ƙaramar hukumar, Adamu Iliyasu Hotoro ya ce Hajiya Shamsiyya Ibrahim wadda mataimakinta, Bello Mustapha, ya wakilta ya bayyana cewa wannan yunƙuri wani ɓangare ne na babban wayar da kai da hukumar NOA ke gudanarwa a faɗin ƙasar nan.

Bello Mustapha ya bayyana cewa wayar da kan yana da nufin ƙarfafa wayar da kan jama’a kan muhimman abubuwa da suka haɗa da manufofin gwamnati, hanyoyin guje wa ambaliya ruwa da shirin dakile hadurran bala’o’i, batun tsaro na ƙasa, da kuma farfaɗo da ɗabi’u da ƙimomin ƙasa. Haka kuma, ana yin cikakken bayani kan shirye-shiryen gwamnati da ake aiwatarwa.

Daga nan ya ƙara da cewa an mayar da hankali musamman wajen daƙile mummunan al’adar “signing out” da ɗaliban sakandire ke yi bayan kammala jarabawa wanda ke ƙara ta’azzara halaye marasa kyau a cikin matasa. 

Wayar da kan ya kuma ƙarfafa gina ƙasaitacciyar shaida ta ƙasa ta hanyar ilimantar da jama’a game da alamomin ƙasa da kuma ayyukan gwamnati da ake ci gaba da aiwatarwa.

A jawabinsa Darakta  na Hukumar NOAɓta kasa reshen jihar Kano  wanda Abba Kyari ya wakilta ya bayyana wasu muhimman tsare-tsaren gwamnatin tarayya da ake isar da sakonninsu a cikin wannan wayar da kan da suka haɗar da: Daidaita canjin kuɗin waje (Eɗchange Rate), ƙarfafa noman zamani,Aiwtar da shirin bayar da rancen karatu ga ɗalibai,Kaddamar da shirin gidajen Renewed Hope a faɗin ƙananan hukumomi.

Da yake jawabinsa Hakimin Tarauni, Dan Lawan Kano, Alhaji Bello Ado Bayero wanda Dagacin ƙauyen Alu, Alhaji Kabiru Muhammad, da Hakimin Gundumar Darmanawa Alh Mujitaba Abba Abubakar Wanda ya sami wakilcin Dagacin Darmanawa Umar Bello, sun yi kira ga iyaye, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki da su mara wa wannan yunƙuri baya, musamman domin dakile yawaitar bukukuwan murna marasa tsafta da daliban sakandire ke yi bayan kammala karatu. 

Sun bayyana irin waɗannan al’adu da cewa suna cutar da tarbiyyar yara da kuma dabi’un al’umma gaba ɗaya, kuma suna buƙatar a ɗauki mataki nan take.

Yayin gangamin wayar da kai tawagar hukumar NOA ta gudanar da wasu muhimman ayyuka waɗanda suka haɗa da ziyarar girmamawa zuwa fada,yin faɗakarwa a tasha ta Unguwa Uku, Zanga-zangar bayyana ra’ayi da ganawa da masu ruwa da tsaki, ziyarar makarantu don wayar da kan ɗalibai kan kafafen sada zumunta na musamman a cikin ƙaramar Hukumar Tarauni, tattaunawa da ƙungiyoyin matasa da na al’umma.

By ukarofi