Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu na kashe maƙudan kuɗaɗe don ganin ta bunƙasa harkar noma da nufin magance matsalar abinci a faɗin ƙasar nan.
Hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Hukumar Gudanarwar Raya Kogunan Haɗeja/Jama’are Inginiya Rabiu Suleiman Bichi yayin buɗe wasiƙun ‘yan kwangila don neman kwangilar gudanar da wasu manyan ayyuka a ɗakin taro na hukumar dake kan titin Maiguri, Hotoro a Jihar Kano.
Bichi ya jaddada ƙudirin gwamnatin tarayya na ganin abinci ya wadata a ƙasar nan wanda hakan ya sa shugaban ƙasa yake sahalewa hukumomin da abin ya shafa kashe maƙudan kuɗaɗe wajen samar da abubuwan da za su taimakawa manoma da nufin bunƙasa fannin.
Ya kuma ƙara da cewa muhimman ayyukan da hukumar za ta fi bai wa muhimmanci a wannan lokacin sun haɗa da gyaran magudanan ruwa, gyaran filayen noma da ma kayayyakin more rayuwa don jin daɗin manoma.
Bichi ya kuma ja hankalin jama’a musammam waɗanda suke zaune a yankunan da suka shafi madatsen ruwa da su ringa kula, domin madatsen ruwa da ake da su gaf suke da cika wanda da zarar adadin ruwa da za su iya ɗauka ya cika za su iya fitar da raguwar. Wanda sakamakon hakan na iya jawo ambaliyar ruwa a waɗannan wurare wanda daga bisani kan janyo gagarumar asarar dukiyoyi wani lokacin ma har da rayuka.
Suma a nasu ɓangaren ‘yan kwangilar da muka zanta da su sun nuna farin cikinsu tare da yi wa Allah godiya a bisa nasarar da suka samu da kuma zaɓar tasu da hukumar gudanarwar ta raya kogunan Haɗeja Jama’are ya yi a matsayin waɗanda za su gudanar da ayyukan. Tare da bada tabbacin ganin za su yi aiki mai inganci don amfananin jama’a.
Taron ya samu halartar ƙungiyoyin sakai, wakilan hukumar yaƙi da tattalin arziki, ƙungiyoyin manoma, ‘yan kwangila daga kamfanoni daban-daban dama ‘yan jaridu, an dai gudanar da taron a ɗakin taro na hukumar kula da raya kogunan Hadeja Jama’a re dake kan titin Maiguri, Hotoro. Kano a satin da ya gabata.
