Gwamnatin Tinubu za ta bada lamunin Naira biliyan 250 ga manoma, inji Shettima

Spread the love

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya bada umarnin a gaggauta sakin lamunin Naira biliyan 250 ga ƙananan manoma a faɗin Nijeriya.

Umarnin, wanda aka bai wa Hukumar Kula da Samar da Abinci ta Fadar Shugaban Ƙasa (PFSCU), na zuwa ne da nufin hanzarta rabon bashin, wanda shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da shi, don bunƙasa noman rani a yayin da ake tsaka da damina don tabbatar da cigaba da samar da wadataccen abinci ba tare da ƙauƙautawa ba.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma gargaɗi hukumar da cewa dole ta gaggauta samar da tsarin aiwatar da rabon lamunin ta inda kudaden za su kai ga manoman da abin ya shafa ba tare da jan ƙafa ba, inda ya ce gwamnati ba za ta lamunci gafara-sa ba ta ga ƙaho ba.

A cewarsa ” Gwamnatin Shugaba Tinubu ta samar da shirin ne don ganin ƴan Najeriya sun amfana akan lokaci ba don ajiyar kudade ba.”

Shettima, wanda ya yaba wa irin gudunmawar da Shugaba Tinubu ya bai wa hukumar PFSCU don yin gyaran-fuska ga tsare-tsaren samar da abinci ba tare da tarnaki ba musamman a ɓangaren sassauta hanyoyin samar da kayan haɗa taki da kafa asusun tallafin Shugaban Kasa.

Ya ƙara da cewa, “idan ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, hukumomi da masana’antu masu zaman kansu za su hada kai, kudirin gwamnati zai samar da ayyukan ci gaban kasa na zahiri cikin ƙanƙanin lokaci.”

Tuni dai gwamnoni da masu ruwa da tsaki da suka sami halartar taron suka yaba da wannan matsayar da gwamnatin ta ɗauka, inda suka ce za su bayar da duk wani goyon baya ga kwamitin shugaban kasar don ganin an samar da tsari mai kyau wajen rabon tallafin.

By Babaji