
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Zaɓe INEC, ta sanar da tantance sababbin jam’iyyu guda 14 yayin da suke jiran ayyana su a matsayin jam’iyyu masu rajista a Nijeriya, lamarin da ya faɗaɗa fagen siyasa a ƙasar.
Kwamishina kuma Shugaban kwamitin Wayar da kan masu zaɓe na INEC, Sam Olumekun ya bayyana haka a wata sanarwa jim-kaɗan bayan wani zama da hukumar da gudanar a Abuja, ranar Alhamis.
Ya bayyana cewa, INEC ya karɓi takardun neman kafa jam’iyya guda 171, waɗanda a yayin tantance su ne aka tabbatar da guda 14 da suka cancanta bisa la’akari da sashe na 222 na dokar ƙasa kundin 1999.
Haka kuma, tuni INEC ta wallafa sunayen jam’iyyun a shafukanta na yanar gizo domin sanar da al’umma.
Jam’iyyun sune kamar haka:
African Transformation Party (ATP)
All Democratic Alliance (ADA)
Advance Nigeria Congress (ANC)
Abundance Social Party (ASP)
African Alliance Party (AAP)
Citizens Democratic Alliance (CDA)
Democratic Leadership Alliance (DLA)
Grassroots Initiative Party (GRIP)
Green Future Party (GFP)
Liberation People’s Party (LPP)
National Democratic Party (NDP)
National Reform Party (NRP)
Patriotic Peoples Alliance (PPA)
Peoples Freedom Party (PFP)
Hukumar ta kuma gayyaci shugabanni da sakatarorin riƙo na masu neman kafa jam’iyyun domin tattauna muhimman al’amura a kansu, inda ta nemi su halarci hedikwatarta da ke Abuja a ranar 17 ga Satumba, 2025.
