Daga ranar Laraba za a fara sayar da tikitin kallon gasar cin kofin duniya, ƙasa da shekara ɗaya da za a yi bikin buɗe wasannin a birnin Mexico.
Ana sa ran kuɗin tikitin zai kama daga matsaikaicin kuɗi dalar Amurka 60 zuwa wasan ƙarshe dalar Amurka 6,730.
Za a fara gasar cin kofin duniya daga 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yulin baɗi.
Kimanin ’yan kallo miliyan 6.5 ake sa ran za su halarci gasar cin kofin duniya da tawaga 48 za ta kece raini a wasa 104 da za a buga tsakanin Mexico da Canada da kuma Amurka
Ranar 5 ga watan Disamba za a fitar da jadawalin gasar cin kofin duniya a Kennedy Center.
