Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙaramar hukumar Faskari da ke Jihar Katsina sun tabbatar da cewa an ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin al’ummar yankin da wasu daga cikin ƴan bindiga da ke addabar yankin tsawon lokaci.
Wannan yarjejeniya ta samu ne a yayin wani zama na musamman da ya gudanar, inda aka cimma matsaya cewa ƴan bindigar za su daina kai hare-hare ko cutar da al’umma, amma za su riƙa shigowa gari don gudanar da rayuwar yau da kullum cikin lumana.
Wannan mataki ya zo ne bayan dogon lokaci na tashin hankali da kashe-kashe da garkuwa da mutane da aka sha fama da su a yankin, wanda hakan ya tilasta wasu al’umma barin muhallansu.
Yayin da wasu ke kallon wannan mataki a matsayin nasara da ci gaba wajen dawo da zaman lafiya, wasu na nuna damuwa kan amincewa da ’yan bindiga su shiga gari ba tare da an hukunta su ba.
Ana sa ran hukumomi za su ci gaba da sa ido kan yarjejeniyar tare da ɗaukar matakin da ya dace don tabbatar da dorewar zaman lafiya a yankin.
An ji babban ƙasurgumin ɗan bindiga Ado Alero ya na tabbatar wa manoma a yankin da su je su cigaba a aikin gonar su ba tare da fargaba ba.
“Daga yanzu kowa ya je gonar sa hankalin sa kwance, babu abinda zai faruwa a duk faɗin ƙaramar hukumar Faskari,”inji Alero.
Ana sa ran hukumomi za su cigaba da sa ido kan yarjejeniyar tare da ɗaukar matakan da ya dace domin ɗorewar zaman lafiya a yankin.
