Tare da BILKISU YUSUF ALI
08054137080, [email protected]
Gabatarwa:
Kurajen fuskar da ake kira da ‘pimples’ a turance na ɗaya daga cikin matsalolin fata da suka fi addabar mutane a duniya, musamman matasa da matan da ke fuskantar sauyin jiki ko ‘hormones’. Wannan cuta tana faruwa ne sakamakon toshewar ‘pores’ na fata da mai da ƙwayoyin fata da suka mutu da kuma wasu ƙwayoyin cuta. Duk da cewa, ba cuta ce mai hatsari ba, amma tana iya haddasa raɗaɗi, kunya da damuwa, musamman idan ta yawaita ko ta bar tabo a fuska.
A cewar Mayo Clinic, ƙurajen fuska na iya tasiri ga kowa maza ko mata kuma yana iya zama tsanani daga ƙarami zuwa mai muni. Yawancin mutane suna neman hanyoyi masu sauƙi, marasa illa da kuma waɗanda ba su da tsada don magance wannan matsala, musamman hanyoyin gida.
A cewar Healthline (2023), yawancin mutane da ke fama da kuraje suna fi son amfani da magungunan gida saboda sauƙin samu, ƙarancin illa, da sauƙin sarrafa su musamman kuma da yawancin magungunan waraka na wannan kurajen na fuska suna sanya sauya fata.
Dalilan da ke haddasa ƙurajen fuska (Pimples):
A cewar Mayo Clinic, akwai dalilai da dama da ke janyo kurajen fuska akwai;
1. Yawan fitar mai (Sebum): Yana haɗuwa da ƙwayoyin fata ya toshe pores.
2. Toshewar pores: Ya haddasa blackheads da whiteheads.
3. Bacteria (Propionibacterium acnes): Yana haddasa kumburi.
4. Sauyin hormones: Yana ƙara fitar mai, musamman a matasa da mata masu ciki.
5. Abinci mai saurin narkewa (high glycemic indeɗ): Kamar farin burodi, shinkafa da sukari.
6. Damuwa (Stress): Yana ƙara cortisol, wanda ke ƙara fitar mai.
7. Kayan gashi da kwalliya masu mai: Na iya toshe pores.
8. Gado (Genetics): Idan iyaye suna da kuraje, kai ma zaka iya samu.
9. Wasu magunguna: Steroids, lithium, da wasu maganin hormones.
10. Wanke fuska da ƙarfi: Yana ƙara fitar mai maimakon ragewa.
Magunguna don magance ƙurajen fuska masu sauƙin haɗawa:
1. Zuma da kirfa (Honey + Cinnamon Mask)
Haɗa zuma cokali 2 da kirfa rabin cokali. Shafa, a barshi minti 10.
2. Aloe Vera
Sanyaya fata, rage kumburi.
Ake shafawa sau biyu a rana.
3. Ruwan lemon (Lemon juice)
Acidic, yana busar da kuraje.
A shafa kan ƙurji kawai na minti 10. A zauna a inuwa kada a fita rana.
4. Kwakwamba (Cucumber Mask)
Rage kumburi, hydration.
A markada, shafa na minti 15.
5. Turmeric da yogurt
Rage inflammation.
A hada kurkum da yogurt a shafa minti 20.
6. Garlic paste
Antibacterial (spot use).
A bar shi minti 5 kawai.
7. Green Tea
Polyphenols suna rage mai da kumburi.
A tafasa, a shafa ko a hada da yogurt a shafa a fuska.
Matakan kariya da hanyoyin hana ƙurajen fuska sake f itowa:
1. Tsabtace fuska da sabulu mai laushi sau biyu a rana.
2. Kayan kwalliya masu “non-comedogenic” kawai.
3. Kula da gashi – kada ya taba fuska.
4. Kar a matsa kuraje – yana haifar da tabo.
5. Sauya pillow da tawul akai-akai.
6. Kada a taɓa fuska da hannu mai ƙazanta.
7. Shan ruwa da cin abinci lafiya.
8. Rage damuwa da bacci mai kyau.
9. Sunscreen mai non-comedogenic.
10. Ganin likita idan kurajen sun yi yawa.
