Yanke wuta ya haifar da mace-mace a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da ke Jihar Kano ya miƙa saƙon neman agajin gaggawa ga Kamfanin Raba Wutar Lantarki na jihar (KEDCO) da ya gaggauta warware matsalar katsewsr wuta a asibitin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar da dama daga cikin marasa lafiya.

A wata sanarwa da Shugabar sashen yaɗa labarai na AKTH, Hauwa Inuwa Dutse ta fitar, hukumar gudanarwar asibitin ta bayyana damuwarta kan yadda hakan ke jefa al’umma cikin ƙunci.

“Hukumar gudanarwar AKTH tana alhinin rasuwar wasu marasa lafiya da ke cikin mawuyacin hali bayan KEDCO ya katse wutar lantarki a baki ɗaya asibitin kan bashin da asibitin yake aiki tuƙuru wajen biya”, inji sanarwar.

Ta yi gargaɗin cewa halin da asibitin ya samu kansa a ciki na rashin lantarki barazana ne ga rayukan musamman marasa lafiya, inda ta ce samar da wutar lantarki abu ne da ke taka muhimmiyar rawa ga ceto rayukansu saboda amfanin lantarki ga na’urorin kula da marasa lafiya.

Haka kuma ta bayyana cewa, AKTH na biyan kuɗin wuta akan ƙa’ida ta kuɗaɗen shiga (IGR) da yake samu, sannan ya kan kashe wasu wajen sayan gas domin sa wa janareto saboda ko ta-kwana.

Don haka hukumar gudanarwar ta yi magiya ga KEDCO da ya tallafa wa ayyukan asibitin akan marasa lafiya ta hanyar dawo da lantarki a yayin da ake ƙoƙarin warware batun bashin da ake binsa.

Wasu jami’an AKTH sun bayyana cewa, ana ƙoƙari wajen ganin an biya bashin tare da gargaɗin matuƙar aka cigaba da katse wutar, to za a cigaba da samun mace-mace a nan gaba.

A hirarsa da manema labarai, mahaifin wani mara lafiya da ke kwance a ɗakin masu dogon suma, Garba Suleiman ya koka ga hukumomin gwamnati da su gaggauta ɗaukar mataki domin ceto rayukan marasa lafiya.

Ya ƙara da cewa, “zuwa yanzu mun binne yara biyu daga wannan rukunin saboda wannan rashin lantarkin. Wajibi ne gwamnati ta yi abinda ya dace domin dakatar da samun maƙabartar marasa lafiyar da suka gaza samun taimako.”

By Babaji