Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kakakin majalisar wakilan Najeriya Hon. Tajudeen Abbas ya ce idan aka yi amfani da basukan da gwamnati ke shi yadda ya kamata za su taimaka wajen bunƙasa ci gaban ƙasar.
Cikin wata sanarwa da kakakin ya fitar bayan taron kwamitocin kuɗi na ƙungiyar Majalisun Dokokin Yammacin Afirka, Hon Tajudeen ya ce idan ba a yi amfani da basukan ta hanyar da ba ta dace ba za su iya jefa ƙasashen cikin matsin tattalin arziki.
“Ya zuwa tsakiyar shekarar 2025, jimillar bashin da ake bin Nijeriya ya kai tiriliyan 149.39 (kimanin dalar Amurka biliyan 97) abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne batun bashin da ake bin ƙasar, wanda a halin yanzu ya kai kusan kashi 52 cikin 100, wanda ya zarce kaso 40 cikin 100 da dokokin mu suka shimfiɗa.
“Wannan ba damuwa ba ne kawai game da kasafin kuɗi, amma rikicin tsarin da ke buƙatar kulawar gaggawa na majalisar dokoki da kuma yin gyare-gyare,” inji Abbas..
Kalaman da suka yi gaggawar haifar da rahotannin kafafen yaɗa labarai da ke nuna Shugaban Majalisar a matsayin wanda ya yi Allah-wadai da karɓar bashin da gwamnati ta yi.
Sai dai kakakin majalisar ya yaba wa gwamnatin Shugaba Tinubu kan abin da ya kira bunƙasa Nijeriya.
”Shugaba Bola Tinubu na aiki ba dare ba rana don ganin ya mayar da Nijeriya kan sabuwar turba ta hanyar dogara da wasu hanyoyin da ba na man fetur ba”, inji shi.
Ya ƙara da cewa, a karon farko cikin gomman shekaru, Najeriya ta cimma kuɗin shigar da ta tsara samu, ba tare da dogara da cin bashi ba.
”Wannan ya tabbatar da cewa idan muka mayar da hankali za mu rage dogaro do basukan waje tare da ingata tattalin arzikinmu”, inji shi.
