
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Juma’a Shugaba Bola Tinubu zai bar Abuja domin zuwa Kaduna, Babban Birnin Jihar Kaduna.
A wata sanarwa daga Kakakinsa Bayo Onanuga, Shugaban ƙasar zai halarci ɗaurin auren Nasirudeen Yari da amaryarsa Safiyya Shehu Idris a yayin ziyarar tasa.
Nasirudeen ɗa ne na Sanata Abdul’azizi Yari, wato wanda ke wakiltar Jihar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawan Nijeriya kuma tsohon gwamnan jihar.
Haka kuma, shugaban zai kai ziyara ga matar marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, A’isha Buhari a gidansu na Kaduna, inji sanarwar.
Sannan, zai koma Abuja a ranar da zarar ya kammala ziyarar.
