Bayan shekaru 62 gwamnati ta dawo da tsarin samar da fasfo na bai-ɗaya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A wani yunƙuri na inganta hanyoyin samar da fasfo, Gwamnatin Tarayya ta soke tsarin samarwa ta ofisoshi daban-daban inda ta fitar da hanya ɗaya tilo da za a riƙa yi, tsarin da aka dawo da shi tun barin sa shekaru 62 da suka gabata.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya sanar da haka a jiya Alhamis yayin ziyarar gani da ido na Cibiyar Samar da Fasfo da aka kammala ginawa a Hedikwatar Hukumar Shige da Fice (NIS) da ke Abuja.

Ya ce, tun a shekarar 1963 da aka kafa NIS, Nijeriya ba ta sake samun tsarin samar da fasfo na bai-ɗaya ba, wanda ya zama ƙalubale wajen mallaka duba da yadda ake samun jinkiri da rashin daidaito a shiyyoyi daban-daban na ƙasar.

Ya bayyana cewa, sabon tsarin na yanzu zai taimaka wajen ƙara adadin fasfo da ake samarwa a kowace rana, inda a baya ana iya samar da 250 zuwa 300 a kullum, amma kuma yanzu za a iya buga guda 4,500 zuwa 5,000 idan an yi sa’o’i biyar ana aiki.

Hakan ya nuna cewa, ƴan Nijeriya za su riƙa samun fasfo cikin sauƙi kuma akan lokaci.

Sannan, ci-gaban zai taimaka wajen samun fasfo cikin mako guda da zarar mutum ya mika buƙatar nema a madadin makonni biyu ko sama da haka a baya.

By Babaji