Mai Tajul’izzi ya halarci gayyatar da Hukumar Tace Fina-finai ta Kano ta yi masa

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Biyo bayan gayyatar Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’ia ta Jihar Kano ta yiwa Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi da lauyansa Abba Hikima kan muhawarar da suka gudanar ba tare da sanin ta ba, Shehi Mai tajul’izzi ya amsa gayyatar Hukumar tare da rakiyar lauya Abba Hikima.

Ta cikin wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar Sani Abdullahi ya aikewa Blueprint Manhaja da yammacin Alhamis, ya ce, zaman da ya gudana a harabar hukumar, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi dokokin hukumar wanda ya haɗa da alaƙar aikin hukumar da su sha’irai, amma Usman Maidubun Isa bai sami damar halarta ba, a ya yin da wakilinsa ya miƙa uzurinsu.

Shugaban kwamitin bincike kan lamarin, Mal. Isha Abdullahi, ya yaba da yadda Shehi Mai tajul’izzi ya girmama gayyatar hukumar a cikin lokaci.

Kazalika, hukumar za ta cigaba da tattaunawa kan batun domin samun daidaito tare da ƙulla alaƙa mai Kyau a tsakanin sha’irai, mabiyansu haɗi da al’ummar Jihar Kano baki ɗaya.

Wannan na daga cikin ayyukan da doka ta ɗorawa hukumar na tace waƙoƙin sha’iran, yin rijista tare da bibiyar aiyukansu a ya yin majalisi.

By ukarofi